Connect with us

Labarai

Wadanda ku ka zaba za su yi muku aiki yadda ya kamata- Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwa jam’iyyar APC ce za ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da kujerun kansiloli 484 a zaben kananan hukumomin ba tare da amfani da tursasa mai zabe ba ko tsoratar da shi.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan jefa kuri’ar sa a rumfar zaben shi mai lamba 008 a garin Ganduje, karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce”Jam’iyya mai mulki za ta lashe dukkanin kujerun la’akari da yawan fitowar jama’a da ya gani a cibiyar”.

A cewarsa, “Fitowar masu kada kuri’a da kuma gudanar da zaben cikin tsari abin birgewa ne, wanda hakan manuniya ce cewa zaben ya samu karbuwa a wurin mutane”. Inji Ganduje.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa gwamnan ya kuma tabbatar da cewa wadanda suka zaba za su yi musu aiki yadda ya kamata.

Labarai

Hana maza shiga gidan aure: Za a koyawa mata aikin gyaran famfo da wutar lantarki

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta kashe Nara miliyan dubu biyu, domin koyar da mata yadda za su yi aikin gyaran wutar lantarki da gyaran famfo.

Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi a jihar Kano, Murtala Sule Garo ne ya bayyana haka, yayin kaddamar da rabon tallafi na Naira dubu goma-goma ga mutane 1000 a karamar hukumar Takai.

Murtala Sule Garo ya ce”Abun takaici ne a ce jihar Kano da ta ke koyi da musulunci a ce idan wata matsala ta faru a cikin gida sai namiji ya shiga gidan matan aure sannan za a iya magance ta”.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara da ta halarci taron ta rawaito mana cewa, mata da dama ne za su ci gajiyar koyon aikin gyaran wutar lantarki da na famfo domin kawo karshen shigar maza cikin gidaje mata.

Continue Reading

Labarai

A samar mana da makarantar kiwo lafiya da sakandire – Shugaban karamar hukumar Takai

Published

on

Shugaban karamar hukumar Takai kuma shugaban shuwagannin kananan hukumomi, Muhammad Baffa ya roki gwamnatin jihar Kano da ta samar da makarantar kiwon lafiya da asibiti da kuma makarantar sakandire a yankin Takai.

Bayanin hakan na zuwa ne ya yin kaddamar da rabon tallafin Naira dubu goma-goma wanda mutane dubu guda za su amfana a karamar hukumar.

Muhammad Baffa ya ce”Kasancewar babu makarantar gaba da sakandire a karamar hukumar ya na kawo koma baya a cigaban karatun ‘ya’yan mu”.

Continue Reading

Labarai

Rashin sana’a: Samari su guji kashewa ‘yan mata kudi – Hafsa Abdullahi Umar Ganduje

Published

on

Mai dakin gwamnan Kano, Hajiya Hafsa Abdullahi Umar Ganduje ta gargadi matasa da su gujewa kashewa ‘yan mata kudi matukar basu da tsayayyar sana’ar da za su aure su.

Hajiya Hafsa Ganduje ta yi wannan gargadin ne yayi rabon jari ga mata 600 da matasa 400 a karamar hukumar Takai a ranar Asabar.

Ta ce”Matasan da su guji baiwa mata kudin da a ka basu, domin idan su ka juya kudin za su sami abun da za su dogara da kan su har su aure ‘yan mata”.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara, ta rawaito mana cewa Hajya Hafsa Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da cewa za ta yi duk mai yuwa wajen ganin an inganta asibitin garin da kuma samar da makarantar kiwon lafiya a karamar hukumar Takai.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!