Connect with us

Ilimi

Ba za mu janye komawa makaranta ba a Kano – Kwamishinan Ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta tabbatar da gobe Litinin 18-01-2021 za a koma makarantu a fadin jihar baki daya.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan ilimi, Muhammad Sunusi Kiro ya fitar da sanarwar, cewa gwamnatin Kano za ta bude dukannin makarantun Firamare da kuma Sakandire a jihar Kano.

Ya kuma ce”Iyayen Yara da su mayar da ‘ya’yan su wadanda suke makarantun kwana a ranar Lahadin nan da mu ke ciki, gobe kuma daliban jeka ka dawo za su koma makaranta, sannan duk wani labarai da yake zagayawa cewa ba za a koma makaranta ba a gobe, zancan ba shi da tushe balle makama. Gwamnatin jihar Kano ba ta da niyar janyewa komawa makaranta a gobe”. A cewar Muhammad Sunusi Kiru.

Ilimi

Kunci da Tsanyawa: A gina mana Kwalejin kiwon lafiya – Dan Majalisa

Published

on

Dan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Kunci da Tsanyawa, Garba Ya’u Gwarmai, ya nemi gwamnatin jihar Kano da ta gina makarantar Kwalejin kiwon lafiya a yankunan su, domin ganin an samu ƙarin malaman kiwon lafiya a faɗin Kano baki ɗaya.

Garba Ya’u Gwarmai, ya bukaci hakan ne yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Ya ce “Samar da makarantar Kwalejin kiwon lafiyar, zai ƙara inganta ilimi tare da samar da ingantaccen ilimin kiwon lafiya a yqnkin karamar hukumar dama yankin Kano ta Arewa“.

Continue Reading

Ilimi

Adaidaita Sahu: An samu karancin fitowar dalibai da malamai a makarantun Kano

Published

on

Makarantu a jihar kano sun fuskanci karancin dalibai da malamai, sakamakon yajin aikin direbobin Adaidaita Sahu suka shiga.

A zagayen da gidan rediyon Dala ya gudanar da safiyar yau Litinin zuwa wasu makarantu, mun tarar har zuwa karfe Goma na safe da yawa daga cikin makarantun babu dalibai da malamai sai ‘yan kalilan, harma a zantawar mu da wata shugabar makarantar firamare ta ce itama sai karfe Tara saura ta samu zuwa makarantar, sabo da rashin abun hawa na Adaidaita Sahu, domin haka yau ko asambile ma basu samu damar yi ba dukda cewar yau Litinin.

Wakilin mu, Ibarahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa tasgaron da yajin aikin na matuka baburan Adaidaita Sahu ya kawo, ya kuma shafi harkokin kasuwanci da ayyuka a hukumomi da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su daban-daban, sakamakon rashin zuwan ma’aikatan a kan lokaci ko kuma rashin zuwan na su ma baki daya.

 

 

Continue Reading

Ilimi

Adaidaita Sahu: Yajin aikin ya shafi daliban mu na jeka ka dawo – KSSSMB

Published

on

Hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano ta ce yajin aikin da aka shiga ya shafi daliban ta na jeka ka dawo duk da cewa harka ta koyo da koyar w aba ta tsaya ba a fadin jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Baba Musa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala a safiyar yau Litinin.

Ya ce,”Mu na fatan wannan abun da aka shiga za a samu daidaito, domin dalibai su koma bakin aiki yadda ya kamata. Kuma batun lalacewar wasu motocin daukar dalbai a Kano, daman dole ne a samu wasu sun lalace  saboda zirga-zirgar yau da kulum, amma kuma wasu sun yi aiki a safiyar Litinin dinnan sun kwashi dalibai sosai, sauran kuma za a yi kokari wajen ganin gwamnati ta gyara motocin daukar daliban da su ka lalace”.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!