Connect with us

Manyan Labarai

Rahoto: Buhari zai ci gaba da samar kayan more rayuwa a Karkara – Sabo Na-nono

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da kokarin samar da kayan more rayuwa a Karkara domin mutane su ci gaba da rayuwa a cikin karkarar maimakon shigowa birni.

Ministan harkokin noman kasar nan Alh Sabo Muhammad Na-nono ne ya bayyana hakan a wajan bude matatun ruwan da za su ringa samar da ruwa lita dubu saba’in da biyar da ma’aikatar gona ta samar a garin Gamoji dake karamar hukumar Gaya da kuma garin Dan ja a karamar hukumar Gezawa.

Ministan wanda daya daga cikin daraktocin ma’aikatar Engr. Olusegun Owolabi ya wakilita, kuma Daraktan dake kula da jihar Kano, a ma’aikatar, Abba Gana Yamani ya yi bayani amadadin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Manyan Labarai

Zamu farfaɗo da masana’antun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano – Kwamishina

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta farfaɗo da masana’antun yin saƙa na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar nan, domin samawa matasa aiki ta yadda za su dogara da kansu.

Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ziyarci masana’antar saƙar kayayyaki ta ƙaramar hukumar Kura yau Laraba, domin duba halin da take ciki tare da duba yadda za’a farfaɗo da ita daga dogon suman da ta yi.

Tun dai a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a shekarar 2014, ne ya samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin Kano da ta ganata ta yi watsi da masana’anatar.

Yayin duba masana’antar Kwamishinan cikinki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kuma bada tabbacin farfaɗo da masana’antar yin saƙar ta ƙaramar hukumar Kura da ma na faɗin jihar nan, domin samawa matasa ayyukan yi.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani babban sakataren ma’aikatar ciniki da masana’antu na jihar Kano, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, farfaɗo da masana’antar ta Kura, na zuwa ne bisa ƙokarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, domin samawa matasa ayyukan yi.

Ya kuma ce yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da masana’antar tsawon lokaci, a yanzu gwamnatin su za ta yi duk mai yiyuwa, domin ganin an ta ci gaba da aiki ka’in da na’in.

Tun dai a shekarar 2014 ne aka samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak, inda gwamnatin Kano mai ci a yanzu ta ce za ta farfaɗo da ita domin samawa matasa aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun ware miliyoyin Kuɗi domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta ware Naira biliyan biyar domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su bisa la’akari da yadda ake samun matsala wajen biyan su kudaɗen su.

Gwamnan Kano ya yi wannan jawabin ne da safiyar yau Laraba, yayin taron majalisar zartarwa da gwamnatin jihar ta saba yi duk sati, domin tattauna batutuwan da suka shafi gwamnatin jihar Kano.

“Za mu tabbatar an biya dukkanin waɗanda suka dace hakkin su na Fansho, domin su samu damar gudanar da sana’o’in dogaro da kai da za su iya riƙe iyalan su, “in ji Gwamnan”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnatin Kano ta ce za ta tabbatar ta magance matsalar rashin ruwa da al’umma suke fuskanta a sassan jihar, domin samar musu da wani sauƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta zartas da hukuncin hallasta yarjejeniyar ƴan kasuwar Sabon Gari da hukumar gudanarwar kasuwar

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 1, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta zartas da hukunci a kunshin wata ƙara wadda Alhaji Musa Yakubu da mutane 7 suka shigar, suna ƙarar hukumar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari da shugaban hukumar.

Tunda farko, masu karar sun garzaya gaban kotun ne domin neman kotun ta tabbatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ƴan kasuwar da hukumar kasuwar.

Masu ƙarar sun bayyana wa kotun cewar, tun a zamanin mulkin Soja suka ƙulla yarjejeniya da hukumar kasuwar a kan za su gina shaguna a filin kasuwar, kuma za su saɓunta biyan haraji bayan shekaru 15, masu ƙarar sun bayyana cewar kafin shekaru 15 din su cika hukumar kasuwa ta karɓe shagunan.

Da take zartas da hukuncin mai Shari’a Dije Aboki Aboki, ta ayyana cewar wannan yarjejeniya da ke tsakanin kungiyar ƴan kasuwar da hukumar kasuwar halastacciya ce kuma kotun ta tabbatar da ita.

A zaman dai mai Shari’a Dije Aboki ta halastawa ƴan kasuwar ta Sabon Gari, a ɓangaren Barkono da gidajen wanka a shagunan da suka mallaka a karkaahin waccan yarjejeniyar.

An kuma ayyana cewar hukumar kasuwar Sabon Gari, da shugaban hukumar za su biya Naira dubu dari biyu ga ƴan kasuwar.

Continue Reading

Trending