Connect with us

Manyan Labarai

Rahoto: Akwai bukatar tsofaffin dalibai su rinka tallafawa makarantun su – Shugaban makaranta

Published

on

Shugaban makarantar Sakandiren Adamu Na’amaji Malam Sadik Garba Adamu Na’amaji dake Gorondutse a jihar Kano ya bukaci kungiyoyin tsofaffin daliban makaranta da su rinka tallafawa makarantun su domin inganta karatun dalibai.

Malam Sadik Garba ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin mu Abba Isah Muhammad yayin kaddamar da ginin masallaci da kungiyar tsofaffin daliban makarantar Sakandiren Adamu Na amaji a makarantar.

Saurari wannan domin jin cikakken rahoton.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa majalisar dokokin jihar ƙunshin Kasafi kuɗin 2025.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatarwa majalisar dokokin jihar sama da biliyan ɗari biyar da arba’in da tara, a matsayin ƙunshin kasafin kuɗin shekarar 2025.

Da yake gabatar da kasafin a ranar Juma’ar 08 ga watan Nuwamban 2024, gwamna Abba Kabir ya tabbatarwa da majalisar cewa wannan adadin kuɗin da aka ware da cewar za’ayi amfani da su ne wajen gudanar da ayyukan ci gaban rayuwar al’umma.

Abba Kabir ya kuma ce daga cikin ayyukan da za’a yi akwai inganta lafiyar al’umma da ilimi da samar da hanyoyi a faɗin jihar Kano, da dai sauran al’amuran more rayuwar al’umma, kamar yadda wakilinmu na majalisar dokokin Kano Umar Abdullahi Sheka ya ruwaito.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta umarci CBN da ya sakarwa ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗen su.

Published

on

Babbar kotun jaha karkashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Musa Ƙaraye, ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN, da ofishin babban akanta na kasar nan daga yin jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da gwamnatin tarayya ke bayarwa.

Cikin wata ƙara wadda shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Kano da mutane shida amadadin ƙungiyar suka shigar.

Waɗanda ake karar dai a gaban kotun sun hadar da babban akanta na kasar nan da kuma babban bankin Najeriya CBN, sai kuma wasu bankuna guda 7 da dukkanin ƙananan hukumomin Kano.

Masu ƙarar ta bakin lauyan su Barrister Bashir Yusuf Tudun Wuzurci, sun bayyana wa kotun cewar idan aka hana ƙananan hukumomin kudadensu hakan zai haifar da koma baya a jahar Kano kuma yin hakan ya saɓawa doka.

Kotun ta amince da dukkan roke-roken masu karar inda aka kùma ayyana cewar kodai babban bankin ƙasa CBN, ko babban akanta na kasar da ragowar waɗanda aka yi karar ko yan korensu cewar kada su yi jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da ake rabawa kowace karamar hukuma.

Kotun ta kuma yi umarni da a aikewa waɗanda ake ƙara kwafin umarnin da ta bayar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar kotun ta sanya ranar 21 ga wannan watan dan sauraren kowanne ɓangaren.

Continue Reading

Manyan Labarai

Muna Allah wa-dai da tsare yaran da gwamnatin tarayya ta kama yayin zanga-zangar tsadar rayuwa  – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta yi Allah wa-dai da matakin gabatar da matasa da yaran nan a gaban kotun tarayya da ke Abuja, waɗanda aka kama a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, a Kano, da Jos da Kaduna.

Gwamnatin tarayya dai tana zargin waɗanda aka kama ɗin ne da zargin cin amanar ƙasa, bayan da take zargin an same su suna ɗaga tutocin ƙasar Rasha a zanga-zangar kawo ƙarshen yunwa da aka gudanar a tsakanin 1 zuwa goma ga watan Agustan 2024.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya shaidawa Dala FM Kano cewar, babu adalci a gabatar da matasan a gaban kotun, kasancewar mafi yawancin su ƙananan yara ne har da ƴan shekaru 14, da 15, da kuma ƴan shekaru 18.

Tasi’u Soja, ya kuma ce tsare yaran da aka yi kusan watanni uku babu adalci a cikin lamarin, yana mai cewa za su yi duk mai yiyuwa don ganin an yiwa yaran adalci.

“Muna kira ga Ƴan Majalisun Arewa, da Sarakuna, da Ƴan Siyasar Arewa da su yi gaggawar ganawa da fadar shugaban ƙasa domin sakin yaran nan duba da take musu haƙƙi da aka yi, “in ji Tasi’u”.

Rahotanni sun bayyana cewar ana tsaka da shari’ar yaran ne a ranar Juma’a 01 ga watan Nuwamban 2024, sai hudu daga cikin su suka faɗi magashiyyan lamarin da mai shari’ar Oboira Egwyatu ya dakatar da shari’ar don duba yaran.

Kotun dai ta sanya yaran a hannu belin ajiye Naira Miliyan goma-goma kowannen su, tare da wanda zai tsayawa kowannen su mai matakin albashi 15, lamarin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin ta ƙalubalanci sharuɗan belin kasancewar ya yi tsauri da yawa tare da rashin adalci a ciki.

A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar iyayen yaran da aka gabatar a gaban kotun tarayya da ke Abuja, Nura Ahmad Muhammad, ya ce talaucin iyayen yaran da kuma rashin kishin ƴan siyasa da masu fada a ji ne yasa ake tuhumar yaransu da laifukan da basu aikata ba.

Continue Reading

Trending