Connect with us

Labarai

Mu guji yin kalaman da ba su dace ba a kafafen sada zumunta – Ƙungiya

Published

on

Shugabar Ƙungiyar Mu yaƙi baɗala a tsakanin ƴan Media dake nan Kano Hajiya Amina Muhammad, ta ja hankalin matasa masu amfani da kafafen sada zumunta da su kaucewa bayyana kalaman da basu dace ba, domin gudun faɗawa cikin matsala.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Amina ta bayyana hakan ne a yayin zantawarta da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ta na mai cewa, “kamata ya yi matasa su ƙara kulawa da shige da ficensu a kafafen sada zumuntar da suke amfani dasu domin gudun gurɓacewa da akan samu a wannan zamani”.

Ta kuma shawarci iyaye da su ƙara kulawa da wayoyin ƴaƴansu domin sanin irin abubuwan da suke yi da su na yau da kullum.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Amina Muhammad ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta ƙara kulawa da masu amfani da kafafen sada zumunta, domin mafi yawan lokuta karancin kulawar da akan yi ga masu amfani da kafafen ne, ake ƙara samun ɓata gari suke gurɓata wasu.

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!