Connect with us

Wasanni

YUMSUK: Health ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta ƴar Tile

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta sashen gudanar da harkokin lafiya ta jami’ar Yusuf Maitama Sule ta zama zakaran gwajin dafi a gasar ƙwallon ƙafa ta ƴar Tile karo na farko da a ka gudanar a jami’ar.
Sashin Health Services ta doke ƙungiyar University Library da ci biyu da nema a wasan ƙarshe da su ka ɓarje gumi a filin wasa na jami’ar dake Kabuga.
Shugaban Jam’iyar, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya mika kofin ga tawagar ƴan wasan tare da sauran shugabanci jami’ar.
Ya kuma yaba yadda a ka gudanar da wasan a tsakanin ma’aikatan jami’ar, inda ya ce “Hakan zai ƙara danƙon zumunci a tsakanin ma’aikatan, kuma za mu ci gaba da ƙarfafa ɓangaren shirya wasanni wato Sports Unit na jami’ar tare da gudanar da wasanni a nan gaba”.Inji Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa.
Shi kuwa wanda ya shirya gasar, mai horaswa Ahmad Surajo, ya ce, “A shirye ƴan wasannin mu su ke su tunkari kowane wasa a nan gaba”.

Wasanni

Major Sunday Cup: Norway Academy ta lashe gasar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Norway Academy ta samu nasarar lashe gasar cin kofin Major Sunady na kakar 2021, a hannun kungiyar kwallon kafa ta Jogana United da ci 3 da 1.

Wasan an fafata shi ne a yammacin ranar Asabar a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari.

Dan wasan Norway Academy, Yamani shi ne ya zura kwallaye 3 rigis a raga.

Continue Reading

Wasanni

Tofa Premier: Kungiyoyi 8 da su ka kai bantan su zuwa gasar

Published

on

Bayan karkare gasar cin kofin ajin mataki rukuni na daya wato Division One da kungiyoyin su ka fafata wanda hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ke shirya wa kungiyoyin.

A yanzu haka kungiyoyi 8 daga ciki sun sami matakin zuwa gasar cin kofin Tofa Premier League wanda za a fara shi nan ba da jimawa ba.

Ga jerin kungiyoyin:

Darmanawa Warriors

Sauna United

Gaida United

Fc Yola

Gwale United

Ja ko Kore FC

One 2 tell ten FC

Pillars U-15.

Continue Reading

Wasanni

Wasan sada zumunta da za a fafata a yammacin ranar Litinin a Kano

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Dorayi Babba Lions za ta kara da Alma Babies Dorayi a filin wasa na Dorayi Babba Lions Arena dake masallacin Juma’a na Dan Sarari dake Dorayi Babba.

Kano Lions Amo Boys za ta fafata da Kofar Ruwa Unite FC a filin wasa na Kano Lions field dake Kofar Na’isa.

Rimin Gado ta yi rashin nasara a hannun Sani Kaita Academy da ci 1 da nema.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!