Connect with us

Labarai

Watan Azumi: Najeriya na bukatar addu’o’in al’umma – SP Abdulkadir

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdulkadir Haruna ya ce, Najeriya na bukatar addu’o’in al’umma, domin samun zaman lafiya mai daurewa tare da taimakawa jami’an tsaro wajen kula da abin da ya ke kewayen da ita.

SP Abdullahi, ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilin mu na ‘Yan Zazu, yayin taron bita da kwamitin masallacin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya shirya ga limaman masallatan shiyyoyin ‘yan sanda dake kananan hukumomi 44 a shelkawatar ta dake unguwar Bompai, domin fadakar da su yadda za su gudanar da wa’azi a cikin watan Ramadan.

Ya ce, “Akwai bukatar kowa ya zama jami’in tsaron kan sa, sannan kuma idan ba ka amince da mutum ba, ka yi gaggawar sanar da hukumar tsaro mafi kusa da kai, domin daukar mataki, saboda samun zaman lafiya a Najeriya mai daurewa”. Inji SP Abdulkadir.

A nasa bangaren, SP Muhammad Kabir Abubakar, babban limamin masallacin ‘yan sanda shiyya ta daya wato Zone One ya bayyana cewar,”Akwai bukatar mutane su san hukunce-hukuncen azumi kafin zuwan sa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, SP Muhammad Kabir ya kuma ja hankalin al’umma da su tabbatar sun sauke nauyi kafin shigowar azumin watan Ramadan.

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending