Connect with us

Labarai

Tsangaya: Turawan Yamma ne su ka hana daukar nauyin almajiri – Malam Idris Rogo

Published

on

Wani malami a tsangayar ilimi da sanin halayyar Dan Adam dake jami’ar Bayero Kano, Malam Idris Rogo ya ce, tsarin tsangaya shi ne yak e samar da mahaddata  alkur’ani a Arewacin Najeriya, tun zamanin baya har zuwa wannan lokacin.

Malam Idris Rogo, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala, yayin taron Kungiyar Al’umma Development Foundation wadda ya gudana a jami’ar Bayero a ranar Alhamis 08-04-2021.

Ya ce, “Saboda wani yanayi da ya zo a yanzu a na fakewa da almajiran tsangayu wajen aikata laifuka, har ta kai ga a na tsangwamar su, kuma babu wani tsari da a ka zo da shi, domin tallafa musu”.

Ya kuma ce, “Tsarin Almajirci a Arewacin Najeriya ya fara ne tun karni na goma sha daya, lokacin Maye Julme na Barno, wanda a tunanin shi ya ware wasu mutanen da za su kula da al’umma, kuma ya fito da tsarin zabo yaran da za a killa ce su, a na ilimantar da su da daukar nauyin su, amma bayan zuwan Turawa su ka hana tsarin na daukar nauyin Almajirai”.  A cewar Malam Idris Rogo.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta rawaito cewar, daga cikin mahalarta taron, Gwani Abubakar Mukhtar Salisu Dala, ya yi fatan tsarin daukar nauyin tsangayun zai sanya yara su haddace Alku’arni mai girma, tun su na shekaru biyar da kuma ilimin sauran litattafan addini.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending