Connect with us

Labarai

HISBAH: Ba za mu laminci Gandaye su rinka cin abinci ba a gaban jama’a

Published

on

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta koka a kan yawaitan rahoto Gandaye wadanda ba sa azumi tare da yin Allah wadarai da halin dabbanci da wani uba ya zakewa ‘yar cikin shi da cewar wai tsautsayi ne.

Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan a ranar Talata 20-04-2021.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya sanya wa hannu, sanarwar ta ce babban kwamandan ya na mai cewar,”Ya zama wajibi, a kan iyaye, da shugabanin jama’a da sauran masu ruwa da tsaki da su hada karfi da hukumar Hisbah, domin magance tabarbarewan tarbiya da kin jin tsoron Allah, domin kai wa ga tudun mun tsira”.

Dr. Harun Ibn Sina ya kara da cewar,”Daga yanzu hukumar Hisbah za ta ci gaba da kai sumame a sako da lunguna na sassan jihar Kano, domin dakile barna da kuma wadan da a ka cafke da laifin cin abinci a cikin jama’a batare da wata kwakwaran dalili ba, kuma za mu tura shi zuwa kotu nan take , domin girbar abun da ya shuka”. A cewar Ibn Sina.

Ilimi

Kai ziyara a ranar Sallar Idi na da muhimmanci a tsakanin al’umma – Limami

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa Mallam Abdulkareem Aliyu ya ce, kai ziyara ga gidajen ‘yan uwa a ranar Sallar Idi abu ne mai matuƙar mahimmanci a rayuwa.

Mallam Abdulkareem ya bayyana hakan ne ta cikin huɗubar Sallar Idi da ya gabatar yau Alhamis a masallacin ga al’ummar Musulmai.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da ya halarci masallacin ya rawaito cewar, Mallam Abdulkareem Aliyu ya kumace, kamata yayi a irin wannan ranaku Musulmai su rinƙa kai ziyarar musamman ma ga gidajen marayu, gakiyayyu, maƙabartu, da gidan masu rangwamin hankali, inda yace kai ziyarar kansa a samu gwaggwaɓan lada ba ka ɗan ba.

Sannan kuma Malamin ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa da yin addu’a domin neman falalar Allah S.W.T

Continue Reading

Labarai

Huɗubar Sallar Idi: Mu rinƙa taimakawa marayu: Muhammadu Sunusi II

Published

on

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na biyu, ya ja hankalin al’ummar musulmai da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin dana zamani, domin  sanin yadda zasu bautawa Allah S.W.T

Muhammadu Sunusi Na biyu ya bayyana hakan ne, a yayin gabatar da huɗubar Sallar Idi da ya gabatar a ranar  Alhamis a Filin Idi na Murtala Muhammad Square dake jihar Kaduna.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu ƙara himma wajen taimakawa marayu tare kuma da sada zumunci a tsakani, domin rabauta da rahamar Allah S.W.T

Wakilin mu Abba Ibrahim Lafazi da ya halarci masallacin a jihar Kadunan, ya rawaito mana cewar, Mallam Muhamadu Sunusi na biyun ya kuma shawarci mutane, da su kaucewa saɓawa Allah S.W.T domin gujewa fushinsa.

Continue Reading

Labarai

Bikin Sallah:  Duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba ma so a kai kasuwa – Samari

Published

on

Yayin da ake shirye-shiryen bikin Sallah karama, samari sun ce duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba su a ciki a kai kasuwa.

Sai dai kuma a hannu guda wasu samarin kuwa cewa su ka yi, duk wacce ta yi kwalliyar abayar mai son kudi ce.

Shi kuwa wani matashi ya bayyana ra’ayin sa ne da cewa, duk wanda baya son mai abayar tsoho ne, saboda haka shi mai abayar ma yafi kauna, saboda ita ce wayayya ‘yar zamani, kuma shi yaro ai da yarinya aka san shi.

Haka zalika, wasu matasan a nasu ra’ayin cewa su ka yi, kwata-kwata ma su ba zu su yi budurwar a lokacin wankan sallar ba, saboda gudun kar su dauki Kucaka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!