Connect with us

Labarai

Kano: Ƴan sanda sun ceto yarinya da iyayen ta su ka tsare ta a gida  shekaru 10

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta Kubutar da wata yar shekaru 15 da haihuwa dake unguwar Darerawa Quarters, karamar hukumar Fagge bisa tsare ta a cikin daki  tsawon shekaru goma 10 da iyayen ta su ka yi babu cikakkiyar kulawa.

Yarinyar mai suna Aisha Jibrin, iyayenta Muhammad Jibrin da Rabi Muhammad, ana zargin sun tsare ta  ba tare da ingantaccen abinci da kiwon lafiya ba sannan basu bayyana dalilin su izuwa yanzu na aikata hakan ba.

Kakakin Rundunar Ƴan Sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewar, Bayan samun rahoton Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tashi tawagar Likitoci da Masu gudanar da binciken ƙwaƙwaf su ka yiwa gidan Ƙawanya domin ceto rayuwar Aisha.

Ya kuyma ce, sun sami nasarar ceto yarinyar tare da garzayawa da ita zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed dake Kano.

DSP Kiyawa, ya kara da cewa, Kwamishinan Ƴan Sanda Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da Umurnin Tsare Mahaifan Yarinyar domin ci gaba da gudanar da binciken Ƙwaƙwaf a babban Sashin Binciken manyan laifuka na rundunar  Ƴan Sandan Kano dake Bompai.

Ilimi

Kai ziyara a ranar Sallar Idi na da muhimmanci a tsakanin al’umma – Limami

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa Mallam Abdulkareem Aliyu ya ce, kai ziyara ga gidajen ‘yan uwa a ranar Sallar Idi abu ne mai matuƙar mahimmanci a rayuwa.

Mallam Abdulkareem ya bayyana hakan ne ta cikin huɗubar Sallar Idi da ya gabatar yau Alhamis a masallacin ga al’ummar Musulmai.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da ya halarci masallacin ya rawaito cewar, Mallam Abdulkareem Aliyu ya kumace, kamata yayi a irin wannan ranaku Musulmai su rinƙa kai ziyarar musamman ma ga gidajen marayu, gakiyayyu, maƙabartu, da gidan masu rangwamin hankali, inda yace kai ziyarar kansa a samu gwaggwaɓan lada ba ka ɗan ba.

Sannan kuma Malamin ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa da yin addu’a domin neman falalar Allah S.W.T

Continue Reading

Labarai

Huɗubar Sallar Idi: Mu rinƙa taimakawa marayu: Muhammadu Sunusi II

Published

on

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na biyu, ya ja hankalin al’ummar musulmai da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin dana zamani, domin  sanin yadda zasu bautawa Allah S.W.T

Muhammadu Sunusi Na biyu ya bayyana hakan ne, a yayin gabatar da huɗubar Sallar Idi da ya gabatar a ranar  Alhamis a Filin Idi na Murtala Muhammad Square dake jihar Kaduna.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu ƙara himma wajen taimakawa marayu tare kuma da sada zumunci a tsakani, domin rabauta da rahamar Allah S.W.T

Wakilin mu Abba Ibrahim Lafazi da ya halarci masallacin a jihar Kadunan, ya rawaito mana cewar, Mallam Muhamadu Sunusi na biyun ya kuma shawarci mutane, da su kaucewa saɓawa Allah S.W.T domin gujewa fushinsa.

Continue Reading

Labarai

Bikin Sallah:  Duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba ma so a kai kasuwa – Samari

Published

on

Yayin da ake shirye-shiryen bikin Sallah karama, samari sun ce duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba su a ciki a kai kasuwa.

Sai dai kuma a hannu guda wasu samarin kuwa cewa su ka yi, duk wacce ta yi kwalliyar abayar mai son kudi ce.

Shi kuwa wani matashi ya bayyana ra’ayin sa ne da cewa, duk wanda baya son mai abayar tsoho ne, saboda haka shi mai abayar ma yafi kauna, saboda ita ce wayayya ‘yar zamani, kuma shi yaro ai da yarinya aka san shi.

Haka zalika, wasu matasan a nasu ra’ayin cewa su ka yi, kwata-kwata ma su ba zu su yi budurwar a lokacin wankan sallar ba, saboda gudun kar su dauki Kucaka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!