Connect with us

Labarai

CPC Kano: An kama lalatacciyar Dusar Dabbobi motar Tirela 4

Published

on

Hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano ta kama lalatacciyar dusar dabbobi kimanin motar tirela hudu da  kuma buhu dari bakwai da saba’in da hudu na gurbataccen takin zamani.

Mai rikon shugabancin hukumar Dakta Baffa Babba Dan Agundi ne ya sanar da haka ga manema labarai ta cikin wata takarda mai dauke das a hannun jami’in hulda da hukumar Musbahu Aminu Yakasai,ta bakin babban mataimaki na musamman ga gwamna a hukumar KAROTA Nasiru Usman Na’ibawa a ofishin sa.

Sanarwar ta kuma ce,  hukumar ta samu nasarar kama wasu kayayyakin amfanin  yau da kullum kimanin katan dubu biyu wadanda su ke gurbatattu da kuma wanda wa’adin amfaninsu ya kare.

Kayayyakin sun hada da magunguna da Taliyar makaroni da Man shafawa da na girki da Ganyen Shayi da abubuwan hada lemo da sauran su.

Ya ce, “An samu nasarar kame kayayyakin daga ranar Juma’a zuwa Litinin din da suka gabata a sakamakon rahotanni da aka samu daga wasu masu kishin jihar Kano da kuma sumame da ake kai wa kasuwanni”.

Shugaban ya ja hankalin ‘yan kasuwa masu irin wannan dabi’a ta sayarwa da al’umma kaya marasa kyau da su ji tsoron Allah musamman a wannan wata mai alfarma da ake neman gafara a wajen Ubangiji.

Hukumar kuma ta rufe wasu wuraren sayar da abinci daban-daban sakamakon rashin takardun shaidar gwajin lafiya ta ma’aikatan su da kuma rashin takardar shaidar wajen kasuwanci.

Wuraren sun hada da gidajen sayar da abinci da na sayar da ruwa da madarar Yoghout da sauransu.

 

 

 

Ilimi

Kai ziyara a ranar Sallar Idi na da muhimmanci a tsakanin al’umma – Limami

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Alaramma Abubakar Ɗan Tsakuwa Mallam Abdulkareem Aliyu ya ce, kai ziyara ga gidajen ‘yan uwa a ranar Sallar Idi abu ne mai matuƙar mahimmanci a rayuwa.

Mallam Abdulkareem ya bayyana hakan ne ta cikin huɗubar Sallar Idi da ya gabatar yau Alhamis a masallacin ga al’ummar Musulmai.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u da ya halarci masallacin ya rawaito cewar, Mallam Abdulkareem Aliyu ya kumace, kamata yayi a irin wannan ranaku Musulmai su rinƙa kai ziyarar musamman ma ga gidajen marayu, gakiyayyu, maƙabartu, da gidan masu rangwamin hankali, inda yace kai ziyarar kansa a samu gwaggwaɓan lada ba ka ɗan ba.

Sannan kuma Malamin ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa da yin addu’a domin neman falalar Allah S.W.T

Continue Reading

Labarai

Huɗubar Sallar Idi: Mu rinƙa taimakawa marayu: Muhammadu Sunusi II

Published

on

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na biyu, ya ja hankalin al’ummar musulmai da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin dana zamani, domin  sanin yadda zasu bautawa Allah S.W.T

Muhammadu Sunusi Na biyu ya bayyana hakan ne, a yayin gabatar da huɗubar Sallar Idi da ya gabatar a ranar  Alhamis a Filin Idi na Murtala Muhammad Square dake jihar Kaduna.

Ya kuma yi kira ga al’umma dasu ƙara himma wajen taimakawa marayu tare kuma da sada zumunci a tsakani, domin rabauta da rahamar Allah S.W.T

Wakilin mu Abba Ibrahim Lafazi da ya halarci masallacin a jihar Kadunan, ya rawaito mana cewar, Mallam Muhamadu Sunusi na biyun ya kuma shawarci mutane, da su kaucewa saɓawa Allah S.W.T domin gujewa fushinsa.

Continue Reading

Labarai

Bikin Sallah:  Duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba ma so a kai kasuwa – Samari

Published

on

Yayin da ake shirye-shiryen bikin Sallah karama, samari sun ce duk budurwar da ta yi kwalliyar abaya ba su a ciki a kai kasuwa.

Sai dai kuma a hannu guda wasu samarin kuwa cewa su ka yi, duk wacce ta yi kwalliyar abayar mai son kudi ce.

Shi kuwa wani matashi ya bayyana ra’ayin sa ne da cewa, duk wanda baya son mai abayar tsoho ne, saboda haka shi mai abayar ma yafi kauna, saboda ita ce wayayya ‘yar zamani, kuma shi yaro ai da yarinya aka san shi.

Haka zalika, wasu matasan a nasu ra’ayin cewa su ka yi, kwata-kwata ma su ba zu su yi budurwar a lokacin wankan sallar ba, saboda gudun kar su dauki Kucaka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!