Connect with us

Labarai

Karya a lokacin zance na janyo saurin mutuwar aure – Mai Diwani

Published

on

Wani malamin Addinin musulunci a jihar Kano Malam Aminu Mai Diwani,  ya yi kira ga al’umma,   idan sun tashi yin aure su kaucewa yin karya, domin gudun fuskantar matsala a cikin rayuwar auren su.

Malam Aminu yayi kiran ne a yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Yace, “Mafi yawan lokuta karyar da mutane ke yi lokacin da suke neman aure,  ke janyo saurin mutuwar aure”.

Ya kuma ce, “Kamata ya yi ma’aurata su rike aure da muhimmanci tare  da sanya gaskiya da rikon amana”. Inji Malam Aminu Mai Diwani.

Wakiliyar mu Yusrah Ismail Zubair ta rawaito cewa, Malam Aminu Mai Diwani,  ya kuma ja hankalin samari da ‘yan mata,  da su kaucewa yin karya a yayin da suke neman aure.

Labarai

Rahoto: Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye Gangar Ruwa, Malam Zubairu Almuhammady, ya ce Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu, domin ya na daga fifikon sa, ya na gani ta bayan sa kamar yadda ya ke gani ta gaban sa.

Malam Zubairu ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, Dukkanin halittun duniya su na bayan manzon Allah (S.A.W), saboda haka al’umma mu yi koyi da shi, domin haduwa da Allah lafiya.

Domin jin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ubangiji ya yi wa Annabi darajar da babu wanda ya ke da ita – Limamin Maidile

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Jami’u, Sheikh Aliyul Qawwas dake unguwar Maidile a karamar hukumar Kumbotso, Malam Muhammad Kamaludden Abdullahi Maibitil, ya ce manzon Allah (S.A.W) shi ne shugabannin dukkanin Annabwa, kuma ubangiji ya girmama shi da girman da ya kadaita shi a kan Annabin kadai.

Muhammad Kamaludden, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa gidan rediyon Dala FM, karin bayani kan abin da hudubarsa ta kunsa.

Domin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai hakuri zai rabauta da rahamar Ubangiji – Limamin Bachirawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Malam Adamu Babarbare dake unguwar Bachirawa, Malam Muhammad Yakubu Madabo, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kasance masu hakuri da juriya a cikin rayuwar su, domin rabauta da falalar ladan masu hakuri.

Malam Muhammad, ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, masu hakuri za su rabauta a duniya da lahira, domin Allah ya tabbatar da zai jarrabi bayin sa, amma idan su ka yi hakuri za su dace da rahamar sa.

Mu na da cikakken bayanin hudubar ta cikin wannan murya dake kasa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!