Connect with us

Labarai

Bai kamata matasa su zauna babu neman ilimi ba – Malam Kamilu Yalo

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na unguwar Ɗorayi Salanta dake yankin ƙaramar hukumar Gwale Malam Kamilu Sheikh Abdulmumin Yalo, ya ja hankalin matasa da su ƙara duƙufa wajen neman ilmin addini da na zamani, domin rayuwarsu ta zama abar koyi.

Malam Kamilu ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Ya na mai cewa, “Bai kamata ace matasan su zauna  ba tare da neman ilmi ba, domin fita daga cikin duhun jahilci”. A cewar Malam Kamilu.

Ya kuma shawarci iyaye, da su kara himma wajen ziyartar makarantun ‘ya’yansu, domin kara karfafawa ya’yan nasu gwiywa wajen koyarwa.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, Malam Kamilu Sheikh Abdulmumin Yalo, ya kuma shawarci iyaye, da su kara bayar da himma wajen kulawa da karatun ya’yansu, domin gudun lalacewar tarbiyyarsu.

Labarai

Rahoto: Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye Gangar Ruwa, Malam Zubairu Almuhammady, ya ce Annabi (S.A.W) zababbe ne a cikin halittu, domin ya na daga fifikon sa, ya na gani ta bayan sa kamar yadda ya ke gani ta gaban sa.

Malam Zubairu ya bayyana hakan ne a hudubar Juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, Dukkanin halittun duniya su na bayan manzon Allah (S.A.W), saboda haka al’umma mu yi koyi da shi, domin haduwa da Allah lafiya.

Domin jin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ubangiji ya yi wa Annabi darajar da babu wanda ya ke da ita – Limamin Maidile

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Jami’u, Sheikh Aliyul Qawwas dake unguwar Maidile a karamar hukumar Kumbotso, Malam Muhammad Kamaludden Abdullahi Maibitil, ya ce manzon Allah (S.A.W) shi ne shugabannin dukkanin Annabwa, kuma ubangiji ya girmama shi da girman da ya kadaita shi a kan Annabin kadai.

Muhammad Kamaludden, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa gidan rediyon Dala FM, karin bayani kan abin da hudubarsa ta kunsa.

Domin cikakken bayanin hudubar saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai hakuri zai rabauta da rahamar Ubangiji – Limamin Bachirawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Malam Adamu Babarbare dake unguwar Bachirawa, Malam Muhammad Yakubu Madabo, ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kasance masu hakuri da juriya a cikin rayuwar su, domin rabauta da falalar ladan masu hakuri.

Malam Muhammad, ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar juma’a da ya gabatar ya na mai cewa, masu hakuri za su rabauta a duniya da lahira, domin Allah ya tabbatar da zai jarrabi bayin sa, amma idan su ka yi hakuri za su dace da rahamar sa.

Mu na da cikakken bayanin hudubar ta cikin wannan murya dake kasa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!