Connect with us

Addini

Islamiyyar mu na bukatar tallafin gwamnati – Anwarudden Islamiyya

Published

on

Limamin masallacin juma’a na unguwar Rugafada a karamar hukumar Kumbotso, Mallam Ayuba Abubakar, ya gargaɗi iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴan su.

Mallam Ayuba Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin saukar karatun Alkur’ani mai girma na ɗalibai 21, na makarantar madarasatul Anwarudden Islamiyya ta gudanar a cikin unguwar Rugafada dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce”Kara kulawa da karatun ƴaƴan na su, zai taimaka mu su a cikin al’amuran rayuwar su ta yau da kullum”. Inji Mallam Ayuba.

Da yake nasa jawabin, mai kula da ɗaukar ɗalibai a makarantar, Mallam Ibrahim Bala Usman, kira ya yi ga gwamnati da masu hannu da shuni, da su tallafa mu su da abun da ya sawwaƙa.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, al’umma da dama ne suka samu damar halartar saukar, daga ciki kuwa akwai dagacin garin Rugafada da ya samu wakilcin, Mallam Alhassan Ali Dahiru, da kuma Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso, Alhaji Muddaseer Ibrahim Zawaciki.

Addini

Muharrami: Ku dai na bari a na shiga gidajen ku – Dan Baito

Published

on

Lauya mai zaman kansa dake jihar Kano, Umar Usman Ɗan Baito, ya shawarci magidanta, da su kaucewa barin mazajen da ba maharramin su ba, shiga gidajen su, domin gudun fuskantar matsala a rayuwar auren su.

Barista Umar Usman ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Ƙaddara Ko Ganganci na nan gidan rediyon Dala FM Kano, wanda ya gudana a yammacin Asabar ɗin da ta gabata.

Ya ce”Bai kamata magidanta su rinƙa barin kowanne mutum ya rinƙa shiga gidan na su ba, wai da sunan ɗan uwan su ne, bayan kuma bai cancanta ya shiga ɗin ba”. A cewar Usman.

Da yake nasa jawabin Mallam Naziru Datti Yasayyadi, kira ya yi ga al’ummar Musulmai, cewa idan za su yi aure su rinƙa yawaita addu’o i, domin neman dacewa a wajen Allah (S.W.T).

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya labarto mana cewa, Mallam Naziru Yasayyadi, ya kuma shawarci ma’aurata, da su ƙara himmatuwa wajen jan matan su a jiki, domin ƙara karfafa alaƙar dake cikin rayuwar auren su.

Continue Reading

Addini

Rahoto: Mu koma ga Allah domin samun sauƙin rayuwa – Limamin Masjidul Ƙuba

Published

on

Na’ibin Limamin masallacin juma’a na Masjidul Ƙuba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar birni a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ja hankalin al’ummar musulmi, da su koma ga Allah wajen nisantar abin da Allah ya hana su da kuma yin abin da ya umarce su, domin fita daga cikin halin da a ke ciki.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu na Ƴan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soronɗinki, jim kaɗan bayan idar da Sallar juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Addini

Rahoto: Limamai sun caccaki masu tsokanar mata masu Abaya

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Umar Sa’id Tudun wada dake unguwar Tukuntawa gidan rediyon Manoma, Dakta Abdullahi Jibril Ahmad Ya ce, Laifi ne babba ya kasance mata su rinka fita waje ba tare da sun sanya hijabi ko Abaya ba, saboda akwai izgili ga addini a wayi gari yanzu ana tsokanar matan da su ka saka rigar Abaya.

Dakta Abdullahi Jibril Ahmad, ya bayyana hakan ne a cikin hudubar da ya gabatar ya na bayyana cewar, Matan da su ke sanya Abaya dokar Allah su ka bi, domin duk wadda ta fito cikin shigar mutumci hakan na nuna salihar mace ce.

Domin jin cikakken bayanin saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!