Connect with us

Ilimi

Liman: Mu ƙara ƙaimi wajen yin Nafilfili a kan sace-sace da kashe-kashe – Amirul Jaish

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Amirul Jaish, Aminu Abbas Gyaranya ya ce, al’umma su ƙara ƙaimi wajen yin Nafilfili da kuma Istigfari domin fita daga cikin halin kashe-kashe da kuma sace-sace da ake fama da su.

Aminu Abbas Gyaranya, a cikin huɗubar sa ya bayyana cewar, Allah ba ya canja wa, sai  dai al’umma sun canja, saboda sai mun koma ga Allah sannan za mu samu sauƙin masifun da muke fama da su.

Domin jin cikakken bayanin huɗubar saurari wannan.

Addini

Muharrami: Ku dai na bari a na shiga gidajen ku – Dan Baito

Published

on

Lauya mai zaman kansa dake jihar Kano, Umar Usman Ɗan Baito, ya shawarci magidanta, da su kaucewa barin mazajen da ba maharramin su ba, shiga gidajen su, domin gudun fuskantar matsala a rayuwar auren su.

Barista Umar Usman ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Ƙaddara Ko Ganganci na nan gidan rediyon Dala FM Kano, wanda ya gudana a yammacin Asabar ɗin da ta gabata.

Ya ce”Bai kamata magidanta su rinƙa barin kowanne mutum ya rinƙa shiga gidan na su ba, wai da sunan ɗan uwan su ne, bayan kuma bai cancanta ya shiga ɗin ba”. A cewar Usman.

Da yake nasa jawabin Mallam Naziru Datti Yasayyadi, kira ya yi ga al’ummar Musulmai, cewa idan za su yi aure su rinƙa yawaita addu’o i, domin neman dacewa a wajen Allah (S.W.T).

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya labarto mana cewa, Mallam Naziru Yasayyadi, ya kuma shawarci ma’aurata, da su ƙara himmatuwa wajen jan matan su a jiki, domin ƙara karfafa alaƙar dake cikin rayuwar auren su.

Continue Reading

Addini

Islamiyyar mu na bukatar tallafin gwamnati – Anwarudden Islamiyya

Published

on

Limamin masallacin juma’a na unguwar Rugafada a karamar hukumar Kumbotso, Mallam Ayuba Abubakar, ya gargaɗi iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴan su.

Mallam Ayuba Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin saukar karatun Alkur’ani mai girma na ɗalibai 21, na makarantar madarasatul Anwarudden Islamiyya ta gudanar a cikin unguwar Rugafada dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce”Kara kulawa da karatun ƴaƴan na su, zai taimaka mu su a cikin al’amuran rayuwar su ta yau da kullum”. Inji Mallam Ayuba.

Da yake nasa jawabin, mai kula da ɗaukar ɗalibai a makarantar, Mallam Ibrahim Bala Usman, kira ya yi ga gwamnati da masu hannu da shuni, da su tallafa mu su da abun da ya sawwaƙa.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, al’umma da dama ne suka samu damar halartar saukar, daga ciki kuwa akwai dagacin garin Rugafada da ya samu wakilcin, Mallam Alhassan Ali Dahiru, da kuma Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso, Alhaji Muddaseer Ibrahim Zawaciki.

Continue Reading

Ilimi

Liman: Matasa ku aikata abubuwan alheri kafin lokaci ya kure muku – Jami’u Rasul

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Jami’u Rasul dake unguwar Tukuntawa gidan Maza a karamar hukumar birni a jihar Kano, Malam Abubakar Ahmad Soronɗinki, ya yi kira ga matasa da su ribanci lokacin samartaka wajen aikata abubuwan alheri kafin lokaci ya ƙure musu.

Malam Abubakar Ahmad Soronɗinki, ya bayyana hakan ne ta cikin huɗubar juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken bayani kan huɗubar saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!