Connect with us

Labarai

Iyakacin Kwankwasiyya Naibawa a 2023 – Aminu Mai Dawa

Published

on

Guda daga cikin mabiya jam’iyyar PDP tsagin Ambasada Aminu Wali, ya ce sun gama shiryawa tsaf, domin fatattakar tsagin Kwankwasiyya daga cikin jamiyyar.

Aminu Mai Dawa Fagge ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa Hangen Dala na Dala FM, inda ya ce matukar za a ci gaba da tafiya a tsarin da suka dauko, babu makawa jam’iyar za ta shafe tarihin Kwankwasiyya.

Ya ce”Tun tuni mun fara shirye-shiryen da za mu tunkari zaben 2023, inda za mu hade da ragowar bangarori jam’iyyar, domin dai korar tsagin Kwankwasiyya. Domin mu ne ‘yan asalin jamiyyar PDP, saboda kuwa Kwankwasiyya kungiya ce kawai ba jam’iyya ba, domin haka ma a jira zuwa 2023 iyakacin Kwankwasiyya Naibawa”. Aminu Mai Dawa.

Aminu Mai Dawa Fagge wanda tsohon mabiyin jam’iyyar PDP tsagin Kwankwasiyya ne, daga bisani ya koma bangaren Ambasada Aminu Wali.

 

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending