Connect with us

Ilimi

Huduba: Mu nemi ilimi ko a ina ya ke – Limamin Madina

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Madina da ke kasar Saudiyya, Sheikh Abdullahi Bin Abdulrahman, ya ce ilimi na da babban matsayi a Duniya da Lahira.

Shekh Abdullahi Bin Abdulrahman ya bayyana hakanne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Juma’a na Madina.

Ya ce”Hakika an daukaka dan Adam da ilimi ne, mu tsaya kai da fata wajen neman ilimi ko a ina ya ke”. Inji Liman Abdullahi.

Ilimi

A duba halin da daliban Kano ke ciki a makarantar Law – NAKLAWS

Published

on

Shugaban kungiyar daliban shari’a ta kasa reshen jihar Kano (NAKLAWS), Kwamred Khalifa Sa’idu Magaji, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta yi duba kan halin da daliban bangaren shari’a ke ciki na zuwa makarantar Law School.

Kwamred Khalifa Sa’idu, ya bukaci hakan ne yayin da kungiyar ta kai ziyara ofishin magatakardar babbar kotun jihar Kano.

Ya kara da cewar”Kimanin shekaru 6 kenan daliban bangaren shari ‘a ba su sami wani tallafi ba daga gwamnatin jiha, wanda hakan ya kawo koma baya a bangaren”. Inji Kwamrade Khalifa.

A na sa jawabin magatakardar babbar kotun jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ado Bayero ya ce”Ma’aikatar shari’a za ta duba taimakon da za ta yi tare da jan hankalin daliban su mayar da

hankali a kan karatun su. Kuma dalibai ku zama ma su jajircewa a duk inda kuka tsinci kan ku”.

Continue Reading

Ilimi

Ranar malami ta duniya: Rashin ciyar da malamai gaba shi ne matasalar mu a Kano

Published

on

Shugaban kungiyar malaman makarantun Firamare da na Sakanadire (NUT) na jihar Kano, kwamared Muhammad Hambali ya ce, rashin ciyar da malamai gaba shi ne ya ke ci musu tuwo a kwarya.

Kwamared Hambali ya bayyana hakan ne yayin taron bikin ranar malamai ta duniya na wannan shekarar 5 ga watan Oktoba, wanda bikin ya gudana a dakin rufaffen filin wasa na Kofar Mata.

Ya ce”Kamata ya yi gwamnati ta rinka daga darajar likafar malaman a kan lokaci, saboda an fi fuskabtar matsala daga bangaren malaman Firamare”. Inji Kwamrade Hambali.

wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito mana cewa, shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, Kwamared Kabir Ado Minjibir kira ya yi ga gwamnatin jihar Kano, da ta kara kaimi wajen inganta rayuwar ma’aikata, musamman malaman makarantu.

Continue Reading

Ilimi

Rahoto: Gidauniyar Abdullahi Ganduje AHUG ta tallafawa matasa 600

Published

on

Gidauniyar Abdullahi Healthcare Awarenes Ganduje (AHUG), ta tallafawa matasa 600 da ilimin karatun na’urar Komfuta kyauta a yankin karamar hukumar birni a jihar Kano.

Taron wanda ya wakana a karamar hukumar birni a karshen makon da ya gabata, an yaye matasan ne tare da basu horo na sana’a, domin kawar da kwacen waya da kuma harkokin shaye-shaye a tsakankanin matasa a Kano.

Domin jin cikakken rahoton saurari Tijjani Adamu.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!