Connect with us

Labarai

Hatsari: Hukumar kashe gobara ta tabbatar da mutuwar mutane 2

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane biyu daga cikin mutane biyar da hatsarin wata ƙaramar mota da kuma baburin Adai-daita Sahu ya rutsa dasu.

Mai magana da yawun hukumar, SFS Saminu Yusif Abdullahi ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewa, “Bayan faruwar hatsarin a unguwar Millar road ne, jami’an mu su ka kai agajin gaggawa, inda suka deɓi waɗanda hatsarin ya rutsa dasu zuwa Asibitin Sir Muhammadu Sunusi   ba su agajin likitoci, wanda Likitocin su ka tabbatar da rasuwar biyu daga cikinsu”. A cewar SFS Saminu.

SFS Saminu Yusuf, ya kuma gargaɗi matuƙa ababen hawa, da su ƙara kulawa yayin gudanar da tuƙin su, domin gudun afkuwar haɗurra.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, mutanen da likitocin su ka tabbatar da mutuwar su. sun haɗar da Mustapha Sani da Shamsu Bala, yayin da sauran mutane uku su ke samun kulawa daga Likitoci.

 

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!