Connect with us

Labarai

Makarantun al’umma: Saboda karbar kudi mu ka janye malaman mu – Kiru

Published

on

Kwamishinan ilimin jihar Kano Muhammad Sunusi Kiru ya ce, sun  janye malaman Gwamnati daga makarantun al’umma ne, saboda yadda su ke karbar kudade a hannun iyayen yara kuma suna amfani da malaman Gwamnatin.

Kwamishinan ilimin ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da gidan radiyon Dala a Litinin yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Ya ce, “Duk wanda zai kafa irin wannan makarantun, dola ne yabi dokokin  da Gwamnati ta kafa”.

Ya kuma ce, “Kada wanda ya kara baiwa wani mutun kudin hayar Shagunan dake jikin makarantu, matsawar ba gwamnati ba”. Inji Muhammad Sunusi Kiru.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewar, kwamishinan ilimin Muhammad sunusi Kiru, ya kuma kara da cewa, ba za a kara samun irin jinkirin da aka samu ba a jarrabar NBAYIS duba da gyare-gyaren da suka yi.

 

 

 

 

 

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending