Connect with us

Labarai

Kotu ta tura wani mutum zuwa gidan gyaran hali saboda cin amana

Published

on

Wani mutum mai suna, Isma’il Muhammad Zangon Dakata ya gurfana a gaban kotun shari’ar musulunci da ke zaman ta a PRP Kwana Hudu karkashin, Alkali Isa Rabi’u Gaya da tuhumar sa da cin amana d cuta, laifukan da su ka saba da sashi na 203 dana 206, na kundin tafikar da shari’ar musulunci na jihar Kano.

Kunshin tuhumar ya nuna cewa, wani mai suna Bashir Muhammad, dan garin Bidda ta jihar Naija ne ya ba shi a jiyar shinkafa samfafera buhu Dari Biyu da Hamsin, wanda kudin ya kai Naira Miliyan Uku da Dubu Dari da Hamshin, sai dai bayan dansanda mai gabatar da kara, Detective Aliyu Abidin Murtala ya karanta masa kunshin tuhumar ya amsa, amma dai ya ce miliyan Uku ya Sani.

Mai gabatar da kara ya roki kotun da ta bashi rantsuwar kore tuhuma a kan Dubu Dari Biyar din da ya ke musu, ta kuma amsa an kuma bashi rantsuwar a cikin kotun, Daga nan kuma kotun ta yi hukunci, inda a laifin farko na cin amana ta daure shi shekara Uku ko zabin biyan tarar NairaDubu Ashirin, laifin cuta kuma daurin shekara biyu ko tarar Naira Dubu Ashirin, sannan zai biya rankon Naira miliyan Uku.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, kotun ta ce hukuncin daurin zai tafi ne a tare.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!