Connect with us

Labarai

NDLEA: Mu na kokarin kawar da bata garin cikin mu – Isa Likita

Published

on

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a jihar Kano (NDLEA), Isa Likita Muhammad ya ce, hukumar ta na bakin kokarin ta wajen boye sirrikan masu bayar da bayanan sirri ga hukumar.

Likita Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da gidan radiyon Dala a safiyar ranar Alhamis 14-10-2021.

Ya ce”Kofar hukumar a bude ta ke ga dukkanin wanda ya ke son bayar da bayanan sirri, mu kuma za mu boye su sunan wanda ya bayar ɗin, domin kaucewa faɗawa cikin matsala, kuma mu na kokarin kawar da bata garin da ke cikin mu, kamar yadda kowace al’umma ke samun bata gari”. A cewar Isa Likita.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, shugaban hukumar ta hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, Likita Muhammad ya kuma ce, yanzu haka hukumar ta shirya kara daukar ma’aikata, domin samun damar dakile bata gari.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending