Connect with us

Labarai

Mun shigar da tsarin duba lafiyar Ido a cibiyoyin lafiya na matakin farko – Tsanyawa

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta ce ta shigar da tsarin duba lafiyar idanu a cibiyoyin duba lafiya na matakin farko, domin rage matsalar rashin gani a tsakanin al’ummar jihar.

Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da manema labarai, a wani bangare na bikin ranar gani ta duniya da ya gudana a ranar Alhamis 14-10-2021.

Wakiliyar mu, A’isha Shehu Kabara ta rawaito cewa, kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar Kano ta ware wasu fanni, domin bayar da magani kyauta wanda suka hadar da duba lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara da cuta mai karya garguwar jiki da manyan hatsari da sauraran su.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!