Connect with us

Labarai

Kotu ta yankewa yaron da ya yi wa yarinya fyade hukunci

Published

on

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 18 karkashin mai shari’a, Maryam Ahmad Sabo, ta hori wani matashin da a ka kama da laifin fyade.

Tun a ranar 2/7/ 2017 gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da matashin mai suna, Munnir Imam, dan shekaru 16 mazaunin unguwar Ja’en da zargin laifin yin fyade ga wata karamar yarinya.

Ma su gabatar da kara sun gabatar da shaidu da sakamakon likitoci, yayin da matashin ya kare kansa kotun ta same shi da laifi.

Mai shari’a, Maryam Ahmad Sabo, ta yi amfani da sashi na 15 na kundin hukunta kananun yara, wanda ya baiwa kotu damar ta soke tuhuma ko ta bayar da zabin tara ga duk wanda a ka samu da laifi, kuma shekarun sa basu kai 18 ba. Ta kuma bukaci a kawo shaida da zai fadi halin Munnir Imam, kuma shaida ya zo kotun ya bayyana cewar, Munniru mutumin kirki ne sannan dalibi ne a matakin babbar sakandire.

Kotun ta hore shi da ya biya tarar Naira Dubu Dari, an kuma umarce shi da ya biya yarinyar Naira Dubu Dari da Hamsin. Idan kuma ya gaza biya zai kwashe shekaru biyar a gidan gyaran hali, kasancewar lokacin da ya aikata laifin bai kai shekaru 18 ba.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!