Connect with us

Labarai

APC Kano: Uwar jam’iyya ce za ta yanke hukunci – APC

Published

on

Uwar jamiyyar APC ta kasa karkashin shugabancin rikon jamiyyar, Mai Mala Buni, ta aiko da kwamitin da zai karbi korafe-korafe a kan zaben shugabancin jam’iyyar APC a Kano, wanda a ka gudanar a ranar 16 ga wannnan watan na Oktoba.
Shugaban babban kwamitin karbar korafe- korafen, Dr. Tony Macfoy, wanda sakataren babban kwamitin karbar korafe- korafen, Dr. Aminu Waziri, ya magantu a madadin sa a ofishin jam’iyar APC a Kano, ya ce, an turo da kwamitin ne, ya ce”Da zarar mun kammala karbar korafe- korafen za mu hada bayanan da rahotannin inda za mu hada, domin mikawa uwar jam’iyyar ta kasa wadda ita ta turo mu ta kuma yanke hukunci”. Inji Dr. Aminu.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir, ta rawaito cewa, sakataren babban Kwamitin ya ce za su kai har ranar Litinin su na karbar koken-koken da ya biyo bayan zaben na shugaban jamiyyar APC a Kano.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!