Connect with us

Labarai

Mai shirin zama Ango: Matashi ya nemi kotu ta kwato masa da N708,500 da ya kashewa budurwa

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulinci mai zaman ta a Rijiyar Lemo karkashin mai shari’a, Aliyu Muhammad Kani, ta sanya ranar 3 ga watan gobe, domin ci gaba da sauraron wata kara wanda wani mutum mai suna, Muhammad Sani ya shigar ya na karar, Malam Surajo Ya’u da mutum daya.

Mai karar ta bakin lauyansa, Barista Nuhu Jafar, ya nemi taimakon Shari’a da ta sanya wanda a ke kara da mutum daya su dawo da wasu kudade da su ka yi alkawarin dawo da su tun a shekarar 2020.

Kunshin da’awar ya bayyana cewar, mai kara Muhammad Sani, ya nemi auren ‘yar gidan wanda a ke kara, kuma magana ta yi nisa daga karshe a ka ce an fasa bashi auren ta. Domin haka ya nemi a dawo masa da wa su kayayyaki cikin abinda ya nemi a dawo masa da su ka hadar da Leshi ruwan hoda mai kimar Naira Dubu 35, sai wani Leshin mai kimar Dubu 35, shi ma ruwan Lemo da kuma wani Leshin wanda ba a fadi kalar sa ba, mai kimar Dubu 25 da wayar salula ta Naira Dubu 50 da hodar shafawa ta Naira 25 da kuma zunzurutun kudi Dubu 397, sai kuma rigar sanyi wadda a ka saya mata ta Dala 281, wadda in a ka canza kudin sun kai Naira Dubu Dari da Arba’in da Biyar. Jimlatan abin da mai kara ya ke nema a biya shi Naira Dubu Dari Bakwai da Dubu Takwas da Dari Biyar (708,500).

Bayan kammala da’awa, lauyan wanda a ke kara Barista Ya’u Abdullahi Umar, ya yi suka a kan cewar da’war ma sam ba ta tsaya ba, domin mai kara ya gaza bayyanawa kotun wannan kayan da kudin ko wane dalili ne ya sanya a ka bayyar da su.

Mai shari’a Aliyu Muhammad Kani, a cikin kwarya-kwaryar hukunci da ya yi ya bayyana cewar, da’awar ma su kara ta tsaya kuma kotu za ta yi mu su shari’a. Daga nan lauyan wadanda a ka yi kara ya nemi a sa masu wata rana, domin yin martani a kan da’awa, sun kuma musanta dukkanin da’awar da a ka gabatar gaban kotu.

Wakilinmu, Yusuf Nadabo Ismail, ya rawaito cewar, lauyan wanda a ka yi kara ya kuma roki kotun da ta ba su damar zaunawa a waje, domin sasantawa kafin waccan rana ta 3 ga watan Disambar 2021

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending