Connect with us

Addini

Daba da Shaye-shaye: Mun shirya wayar da kan matasa – Ƙwamrade Yarima

Published

on

Shugaban Ƙungiyar Annabi ne mafita, Kwamared Muhammad Suraj Yarima Mai Sulke, ya ce, bai kamata matasa su rinƙa sanya kansu a cikin halin shaye-shaye ba, da sunan nuna murna kan faruwar wani al’amari a garesu.

Kwamared Yarima Mai Sulke ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da Dala FM.
Ya ce,”Kamata idan matasa su rinƙa bin hanyoyin da ya dace, a maimakon sanya kai cikin halin shaye-shaye, domin kaucewa faɗawa cikin matsala”.

Ya kuma ce,”Ƙungiyar mu ta Annabi ne mafita, ta shirya wayar da kan matasa wajen ganin sun cire kansu shiga harkokin daba da shaye-shayen da a ke cigaba da fuskanta a wannan zamani ga matasan”. Inji Kwamrade Yarima.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u, ya rawaito mana cewar, A ɓangarensa shugaban kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Global Community for Human Right Network, Ambasada Ƙaribu Yahya Lawan Kabara, ya ce, kamata ya yi iyaye su ƙara kulawa da tarbiyyar ƴaƴansu, domin gudun faɗawarsu cikin wani hali.

Addini

Rahoto: A rinƙa kyautata alwala yadda Manzon Allah (S.A.W) ya yi – Limamin Al-Muntada

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Almundata da ke unguwar Dorayi, a karamar hukumar Gwale, jihar Kano, malam Nura Sani, ya ce, al’umma su rinka kyautata alwala, domin tana daga cikin manyan ibadu da Allah ya shar’anta ga bayinSa.

Malam Nura Sani, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, yayin da yake karin bayani, dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Addini

Rahoto: Mu rinƙa ƙoƙarin zuwa sallar Juma’a a kan lokaci – Limamin hukumar sharia

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na hukumar shari’a ta jihar Kano, Dayyib Haruna Rashid, ya ce, akwai buƙatar al’ummar musulmi, su rinƙa zuwa masallacin Juma’a a kan lokaci.

Malam Dayyib Haruna Rashid, ya bayyana hakan a zantwarsa da walikin mu na ƴan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Addini

Rahoto: Azumin Tasu’a da Ashura na kankare zunuban shekara guda – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a Na Masjidul Ƙuba da ke unguwar Tukunwa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya ce,  Azumin Tasu’a day Ashura Na kankare zunuban shekara guda.

Malam Abubakar Tofa, ya bayyana hakan ne, a zantwarsa da walikin mu Na ƴan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Trending