Connect with us

Labarai

Gobara: Ɗakunan ƙwana da na girki sun kone ƙurmus a Hotoro- SFS Saminu

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da tashin wata gobara a cikin wani gida da ke unguwar Kawon Mai Gari bayan Firamaren unguwar a yankin Hotoro.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SFS Saminu Yusif Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yammacin ranar Laraba 17-11-2021.

SFS Saminu Yusif ya ce”Mun samu kiran gaggawa ne daga wani mutum mai suna, Yahya Muhammad, wanda ya sanar da su tashin gobarar, bayan samun labarin mu ka tura jami’an mu, domin kai agajin gaggawa tare da shawo kan wutar. Mun kuma tabbatar da ƙonewar ɗakunan kwana guda Uku, sai banɗakuna guda uku, da na girki shi ma Uku, tare da wasu ɗakuna guda Biyu”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewar, ga dukkanin wanda ya ga faruwar wani al’amari da ya kamata hukumar ta bada agaji, za su iya kiran waɗannan lambobin 08107888878, ko 07051246833, da 08098822631, da kuma 07026026400.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending