Connect with us

Labarai

Hatsari: An yi gamo tsakanin mai Motar ruwa da mai Babur

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da faruwar wani hatsari tsakanin wata motar ɗaukar ruwa wadda ta daki wani mai babur mai kafa biyu a kan titin Ɗan Agundi.

Mai magana da yawun hukumar, SFS Saminu Yusif Abdullahi ne ya tabbatar da afkuwar hatsarin da yammacin wannan rana ta Laraba.

Ya na mai cewa”Bayan da mu ka samu labarin afkuwar hatsarin ne, jami’an mu su ka halarci wajen wanda mu ka ɗauki mai babur ɗin mai suna, Hamisu Ibrahim, mun kuma same shi a raye, yayin da mu ka kaishi asibitin kwararru na Murtala, domin ba shi agajin gaggawa. bayan da mu ka kai mutumin asibitin ne mu ka miƙa shi a hannun jami’in ɗan sanda mai suna, Sufeta Yakubu Muhammad da ya ke aiki a ofishin ƴan sandan Ƙofar Wambai”. Inji Saminu Yusif.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta kuma ja hankalin matuƙa ababen hawa su ƙara kulawa da ƙa’idojin tuƙi, domin kaucewa afkuwar haɗura.

Labarai

Rahoto: Mu nisanci abinda Allah Ya hana domin samun saukin rayuwa – Limamin Tukuntawa

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa a jihar Kano, Malam Ahmad Ali, ya ce, al’umma su duba tsakanin su da Allah tare da nisantar abinda ya hana, domin saukin tsadar rayuwa.

Malam Ahmad Ali, ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa wakilin mu na ‘yan Zazu,  Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, Karin bayani dangane da abinda hudubar da ya gabatar ta kunsa.

Akwai cikakken bayanin hudubar a muryar da ke kasa.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rubutu na da muhimmanci a mu’amalar bashi – Limamin Bompai

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai, SP Abdulkadir Haruna, ya ce, akwai bukatar mu rinka gudanar da mu’amalar bashi yadda addinin musulunci.

SP Abdulkadir Haruna, yana bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, bayar idar da Sallar Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya yi yunkurin cinye tabar Wiwin da aka kama shi da ita a hanyar kotu

Published

on

Ana zargin wani matashi ya yi yunkurin hadiye tabar Wiwi da miyagun kwayoyi da aka kama shi da ita a hanyar kotu.

Tunda fari jami’an tsaron, sun kama matasahin da zargin samun sa da kayan maye, inda yake boye da wasu basu sani ba, kafin kuma a kai shi kotu, ya ciro su yana yunkurin hadiye wa.

Wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki yana da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending