Connect with us

Labarai

Mai guduwa da wayoyin ƴan mata yayin soyayya ya shiga hannnu

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Muhammad Saifullahi, wanda ake zargin sa da gudar wa ƴan matansa wayoyi idan ya je zance.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama matashin ga manema labarai a daren Talata.

Ya ce, “A makon da ya gabata ne wata budurwa ta shigar da ƙorafin ta kan matashin, wanda ya gudar mata da wayar salula, tare da ta ƙanenta, inda Kwamishinan ƴan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bada umarnin nemansa, yayin da aka kuma samu nasarar kama shi”

Ya kuma ce, “Muna jan hankalin ƴan mata da su ƙara kulawa da irin samarin da za suyi domin gudun haɗuwa da irin wannan saurayi da yake yaudarar ƴan matansa” Inji Dsp Kiyawa.

Matashin da aka kama ɗin da zargin gudarwa ƴan matan nasa wayoyi kusan su huɗu ya ce, “Ina amfani ne da soyayyar da nake yiwa ƴan matan, in gudar musu da waya duk da dai jikina ya ba ni, lokacin kama ni ya zo”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ce, yanzu haka su na ci gaba da faɗaɗa bincike a kan matashin, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu, domin girbar abin da ya shuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!