Connect with us

Labarai

Maukibi: Mutane su yi taka tsantsan yayin bikin – Ƴansanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gargaɗi al’umma musamman ma matasa, da su kaucewa karya doka a lokacin gudanar da bikin Maukibi wanda za a gudanar a ranar Asabar 19-11-2021.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce”Rundunar ba za ta saurarawa dukkanin waɗanda su ka fito riƙe da wuƙaƙe dama dukkanin abin da ya saɓawa doka ba, dukkanin wanda jami’ansu su ka kama ɗin za su ɗauki matakin doka a kansu. Sanin kowa ne jihar Kano za ta samu baƙwancin al’umma daga jihohi daban-daban, saboda haka mu na kira ga al’umma su kaucewa sanya kayan da basu dace da al’ada ba a jikinsu, musamman ma ɗaura zane, sanya sarƙoƙi a jikinsu da kuma askin da bai dace ba, a kasance masu biyayya a yayin bikin Maukibin”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, rundunar ta ce ga dukkanin wanda ya ga faruwar wani baƙon al’amari, zai iya kiran waɗannan lambobin 08032419754, ko kuma 08123821575, domin bayar da agajin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!