Connect with us

Ilimi

Rahoto: Duk harka da ke yi kasuwanci ya sauƙaƙa – SON

Published

on

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta yi iya yin ta wajen taimakawa manoma ta hanyoyin fasaha domin cin gajiyar wayar da kan manoma a fannin harkokin siya da sayarwa.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana hakan ne a lokacin da hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON ta shirya taron bita na wayar da kan manoma da masu siya da sayar, domin saukaka kasuwanci.

Yayin taron shugaban hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON, Salim Farouk, ya ce, a zaman da su ka yi manoma za su gane yadda shinkafa ya ke mai kyau ko mara kyau, wanda dukannin harkokin za su saukaka kasuwanci a kasa baki daya.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya halarci wurin taron, ga kuma rahoton da ya aiko mana daga wajen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Ilimi

Wutar lantarki ce ta haddasa gobara Jami’ar Wudil – SFS Saminu

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da tashin wata gobara a cikin wani gini na sashin kimiyya wanda ya lanƙwame ofisoshi har guda biyar a kwalejin ilmi da fasaha ta Wudil a daren Asabar.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce”Mun samu kira ne daga masu gadin kwalejin, inda mu ka tura jami’an mu ba su yi ƙasa a gwiwa ba su ka kai agajin gaggawa. Al’umma da su ƙara kulawa da yanayin da a ke ƙara tunkara a yanzu”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito mana cewar, hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce binciken su ya gano musu cewa, wutar lantarki itace musabbun tashin gobarar a kwalejin.

Continue Reading

Ilimi

Ilimi: Saukar karatun Kur’ani ba ya nufin dalibi ya gama karatu – Mal Aliyu

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ummul Abdulmalik da ke unguwar Jakara a birnin Kano, Mallam Aliyu Sa’id, ya bayyana cewa, yin saukar karatun Al-ƙur’ani ba shi ne ya ke nuna cewar ɗalibi ya gama karatun Al-kur’anin ba, a lokacin ne ma ɗaliban suka sanya ɗamba.

Mallam Aliyu Jakara ya bayyana hakan ne a yayi saukar karatun Al-ƙur’ani mai girma da makarantar Anas Bin Malik ta gudanar na dalibai 16 cikin unguwar Ja’en da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale.
Ya na mai cewa”Bai kamata dalibai dan sun karɓi Satifiket na sauka, kuma su jingine karatun su ba baki ɗaya, ɗaliban da su kan yi saukar karatun Al-ƙur’ani su ƙara himma wajen yin amfani da abubuwan da a ka koya musu a makaranta”.

Wakilin mu Ibrahim Habibu Abdullahi ya rawaito cewa, Mallam Aliyu Sa’id Jakara, ya kuma ja hankalin ɗaliban da su ƙara himma tare da jajircewa, wajen neman ilimin Alqur’ani mai girma, domin zama abun koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Ilimi

Wasa kwakwalwa: Ɗaliba ta lashe Keke a gasar hada kalmomi na Dawanau

Published

on

Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Ƙwa, ya ja hankalin iyaye da su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, domin rayuwarsu ta zama abar koyi a tsakanin al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana hakan ne ta bakin wakilin sa, Alhaji Sa’idu Abdu Tumfafi a yayin taron gasar Spelling B da Ƙungiyar Ɗalibai da cigaban gari ta Dawanau DASCOSA ta shiryawa Ɗaliban Firamaren Bagadawa dake yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa wanda ya gudana a ranar Alhamis 18-11-2021.

Ya na mai cewa”Matuƙar iyayen za su ƙara kulawa da karatun ƴaƴansu, to kuwa babu makawa za a samu cigaban da ya dace a fannin karatun na su”. Inji Tambai Kwa.
Da ya ke nasa jawabin shugaban Ƙungiyar, Abubakar Tasi’u Dawanau, cewa ya yi, ƙungiyarsu ta shiryawa ɗaliban gasar Spelling B ne, domin ƙarfafa musu gwiwa a fannin karatun su”. Inji Alhaji Sa’idu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, bayan kammala gasar dai an baiwa dalibar da ta zo na farko kyautar Keken ɗinki, sai kuma wacce ta zo ta biyu a ka ba ta kyautar keken hawa, yayin da kuma a ka baiwa dalibin da ya zo na Uku kyautar kuɗaɗe, waɗanda su ka rinƙa bayyana farin cikinsu.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!