Connect with us

Labarai

Kotu ta ayyana bangaren Sanata Shekarau a matsayin halastacce

Published

on

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana zaben shugabanin jam’iya na kananan hukumomi da na jiha wanda bangaren gwamna, Dr. Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC ya gudanar a matsayin haramtacce, mara tushe balle makama.

Alkalin kotun, mai shari’a Hamza Muazu, a hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, ya amince da zaben bangaren, Sanata Ibrahim Shekarau.

Idan ba a manta ba, a ranar 30 ga watan Nuwamba, kotu ta bayyana zarge-zargen da bangaren Abdullahi Ganduje na jam’iyyar ya yi a matsayin haramtacce.

Sai dai a hukuncin na ranar Juma’a, kotun ta kori karar ta su, ta kuma nemi su biya abokan sharia’ar ta su Naira miliyan ɗaya saboda ɓata musu lokaci da suka yi.

Labarai

Ranar ‘yan jaridu ta duniya: Aljanu na satar labarai daga sama – Danfodio

Published

on

Masanin harkokin aljanu a jihar Kano, Abdullahi Idris Danfodio ya ce, aljanu na satar labarai daga sama domin fada wa al’umma.

Abdullahi Idris Danfodio, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Da zarar PI ta fashe za mu yi abinda za mu taimaka wa mutane – Matashi

Published

on

Wani matashi a jihar Kano, Auwal Muhammad Musa, mai jiran fashewar PI ya ce, da zarar ta fashe za su gudanar da abubuwan da za su taimakawa al’umma.

Auwal Muhammad, ya bayyana, ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa masu jiran fashewar PI na fama da matsalar damuwa – Masani

Published

on

Wani masani da ke karatun babban Digiri a jami’ar Bayero, bangaren nazarin halayyar Dan Adam a jihar Kano, Shu’aibu Lawan Matawalle, ya ce, akwai damuwa ga matasan da ke jiran fashewar PI, domin babu wanda yake samun kudi haka kawai ba tare da yayi kasuwanci ba.

Shu’aibu  Matawalle, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo, dangane da yadda matasa ke jiran fashewar PI.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Trending