Connect with us

Wasanni

Premier League: Robertson ya yi sa’ar kafar sa a wajen Kane – Alkalin Wasa

Published

on

Tsohon alkalin gasar Premier, Mark Clattenburg ya soki alkalancin wasan da Tottenham ta buga da Liverpool a ranar Lahadi, ya na mai cewa Andy Robertson ya yi sa’a da ya ci gaba da tafiya.
Harry Kane ya yi wa Robertson wata keta mai karfin gaske wanda ya tsallake rijiya da baya.

Alkalin wasa Paul Tierney ya ba da katin gargadi ne kawai sannan kuma a ka nuna wa Robertson jan kati kai tsaye kan laifin da ya yi wa Emerson Royal wanda VAR ta sake duba shi.

Clattenburg ya ce “Ina ganin ketar da Kane ya yi ta fi na Robertson muni.”

“Idan ba ku yarda cewa wannan kuskure ne bayyananne ba game da Kane, ba ku yin aikin ku daidai.

“Ina jin mu a matsayinmu na alkalan wasa wani lokaci muna da laifin sanin dokokin wasan, amma ba mu fahimci wasan ba.

“VAR ba zai iya samun wannan kuskure ba, alkalan wasa na iya sanin komai, saboda su na kallo.

“Idan har su na cewa sai an dasa kafarsa, wanda hakan wata sabuwa ce a gare ni, idan kafar ta yi tsayi, ’yan kwalliya su na nunawa, ba ta da hankali, ya yi ihuhu, a gare ni, ya jefa lafiyar abokin hamayyarsa cikin hadari.

“Robbo ya yi sa’a a yau ya na ci gaba da tafiya, ya kamata mu kara fahimtar ‘yan wasan kwallon kafa, saboda ba zai bar kafarsa a can ba, me zai hana?

Clattenburg, wanda ya shafe shekaru 13 a matsayin alkalin wasa na gasar Premier daga 2004 zuwa 2017, yanzu ya zama shugaban alkalanci a kasar Girka.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.



Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.



Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending