Connect with us

Manyan Labarai

AFCON: Super Eagles za ta dauki Jose Mourinho – NFF

Published

on

Hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce ta fara tattaunawa da mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AS Roma, Jose Mourinho, domin maye gurbin Ganoht Rohr a Super Eagles.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta NFF, Melvin Amaju Pinnick ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.

Ya ce ”Super Eagles za ta samu sabon koci nan da mako mai zuwa, abun da ke nufin cewa kocin da ke riko a yanzu ba shi zai jagorance ta zuwa gasar cin kofi nahiyar Afrika ta 2021 ba”

Ya kara da cewa,”Ni da kai na na yi magana da Mourinho kan ko zai karɓi aikin, sannan ministan wasanni, Sunday Dare ma ya yi magana da shi domin jin ko ya na da sha’awar aikin”. Inji Pinnick.

Manyan Labarai

Gobara ta ƙone tarin kayayyaki a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Published

on

Wata Gobara ta tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau dake Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa, inda ta ƙone wasu kayayyaki a ɗakin matar sa waɗanda zuwa yanzu ba’a ƙayyade ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga ɗakin Girki na matar tsohon gwamnan Hajiya Halima Shekarau, tun yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta shafi iya daki ɗaya ne a cikin gidan dake Munduɓawa.

A nasa ɓangaren kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce da zarar sun kammala tattara alƙaluma da bincike, zai magantu a nan gaba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa ta Ɗan Agundi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a mahaɗar Ɗan Agundi, da ke ƙaramar hukumar Birni, domin samarwa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Da yake ƙaddamar da aikin a yammacin yau gwamnan ya ce, gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanen lokaci, hakan yasa yanzu gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Har ila yau, gwamnan Abba Kabir, ya kuma ce an samar da hanyoyin da al’umma za su bi, domin samun saukin zirga-zirga har zuwa lokacin da za’a kammala aikin baki ɗaya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce, an samo kanfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanen lokaci, domin ci gaba da gudanar da zirga-zirga akan lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za mu duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin su dan kyautata rayuwar su – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta duba yiyuwar ƙarawa ma’aikatan shara kuɗin alawus ɗin da ake biyan su, domin kyautata rayuwar su kasancewar abin da ake basu bai taka kara ya karya ba.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka yayin ganawa da ma’aikatan kwashe shara a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnati jihar a yau.

Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa bisa ƙorafe-ƙorafen da ma’aikatan shara suka yi na tsaikon da ake samu wajen biyansu kudin alawus din su tsawon watanni.

“Gwamnati za ta yi bincike domin gano inda matsalar tsaikon biyan ma’aikatan kwashe shara take da nufin magance ta cikin gaggawa, “in ji Gwamnan”.

Ya kuma ƙara tabbatar wa da ma’aikatan cewa, gwamnati za ta tabbatar kowane ma’aikacin shara an tura shi aiki kusa da gidan sa domin sauƙaƙa musu kashe kudi a wajen sufuri.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Abba Kabir, ya bai wa ma’aikatan tabbacin gwamnati za ta biyasu dukkanin basukan da suke bi, tare da duba yiwuwar ƙara musu kudin alawus nan bada daɗewa ba.

Continue Reading

Trending