Connect with us

Manyan Labarai

AFCON: Habasha ta kasance ta farko da ta sauka a Kamaru

Published

on

Kasar Habasha ita ce ta farko da ta isa kasar Kamaru, domin buga wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na mai taken TotalEnergies 2021, wanda za a fara ranar 9 ga watan Janairun 2022.

Tawagar ta isa filin jirgin saman Nsimalen na Yaounde a ranar Lahadi 26 ga Disamba. Bayan isowar, ‘yan wasa, ma’aikatan fasaha da masu zartarwa na FA sun yi gwajin Covid-19 a filin jirgin sama kafin su koma otal din kungiyarsu.

Kocin kasar, Wubetu Abate da tawagarsa sun yi atisaye a filin wasa na Ahmadou Ahidjo Annex 1.

Walias sun dawo gasar a karon farko tun 2013. Wanda su ka taba lashe gasar kofin AFCON guda daya, da a ka gudanar a shekarar 1962 a kasar ta.

Habasha ta na cikin rukunin A ne da Burkina Faso da Cape Verde da Kamaru mai masaukin baki.

A ranar 9 ga watan Janairu ne za su kara da Cape Verde bayan wasan farko tsakanin Kamaru mai masaukin baki da Burkina Faso. Habasha za ta kara da mai masaukin baki ne a ranar 2 ga wata kafin a rufe wasannin rukuni-rukuni da Burkina Faso a ranar 17 ga watan Janairu.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending