Connect with us

Manyan Labarai

Kanin Maradona Hugo ya mutu sakamakon bugun zuciya

Published

on

Hugo Maradona wanda kanin fitaccen dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego, ya mutu sakamakon bugun zuciya.

Hugo mai shekaru 52 ya fuskanci mummunan harin ne a gidansa da ke Naples, birnin da Diego ya taka leda a kololuwar rayuwarsa kuma inda Hugo ya taka leda tun ya na karami.
Hugo ya mutu da misalin karfe 11.50 na safiyar Talata.

Hakan na zuwa ne watanni 13 kacal bayan da bugun zuciya ya kashe Diego, gwarzon gasar cin kofin duniya na Argentina kuma daya daga cikin mafi girma da ya taba buga wasan wanda ya mutu a Argentina a watan Nuwamba 2020 ya na da shekaru 60.

An ga Hugo a filin wasa na Maradona da ke Naples, domin halartar bikin tunawa da dan uwansa marigayi kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa wata daya kacal da ya wuce.

Ya bar mace mai suna Paola Morra wadda ya aura a shekara ta 2016, da ’ya’ya uku.
Ƙananan ‘yan’uwan Maradona da sauran su ne Diego da Raul da Hugo shi ma dan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ya sanya hannu a matsayin ƙarami ga kungiyar Napoli mai shekaru 18 a 1987.
Amma ba kamar ɗan’uwansa ba, wanda ya buga mafi kyawun shekarunsa a Napoli kuma a na girmama shi a birnin Naples ta kasar Italiya a matsayin wani abu mai tsarki.

Ranar 20 ga Satumba, 1987, ‘yan’uwan biyu sun yi wasa da juna tare da Napoli ta Diego ta fito a kan 2-1.

Hugo, wanda ya kasance tauraron tawagar Argentina a gasar cin kofin matasa na duniya na FIFA na matasa ‘yan kasa da shekaru 16 a shekarar 1985, wanda ya kasance kan gaba a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 a yau, ya ci gaba da taka leda a kananun gasa na Spain da Austria da Venezuela kafin ya kawo karshen aikinsa na buga wasa a Japan a karshen shekarun 1990.

Bayan haka ya koma horarwa, kuma ya shiga cikin ajin manyan makarantun matasa a matsayin masu horaswa.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending