Connect with us

Manyan Labarai

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada sabon mai horas da Super Eagles

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta sanar da nadin Jose Peseiro, a matsayin sabon mai horas da Super Eagles.

Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta sanar da nadin Peseiro dan kasar Portugal, a matsayin sabon mai hioras da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.
Sai dai hukumar ta NFF ta ce, Augustine Eguavoen, wanda a ka nada kocin rikon kwarya bayan sallamar Gernot Rohr a makonnin da su ka gabata, zai jagoranci Super Eagles zuwa gasar cin kofin Afrika da za a fara ranar 9 ga watan Janairu a Kamaru.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta NFF ta sanar, bayan yin nazari a kan takardar da shugaban kwamitin zartaswa ya gabatar, ya amince da kudirin nada Mista Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles, bayan kawo karshen dangantaka da Gernot Rohr.

Duk da haka, kwamitin ya yanke shawarar cewa, Augustine Eguavoen, wanda ya nada babban kocin rikon kwarya, zai jagoranci Super Eagles zuwa gasar AFCON 2021 a Kamaru tare da Mista Peseiro.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending