Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Afghanistan: Masu aski ku daina askewa mutane Gemu – Taliban

Published

on

Hukumomin Taliban a kasar Afganistan ta haramtawa masu sana’ar yin Aski da su daina askewa mutane Gemun su.
Wannan dokar na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mahukuntan Taliban na Afganistan su ka sanya dokar hana zirga-zirga a kan mata dole sai da muharramin su.

Muryar Amurka ta samu kwafin umarnin da ma’aikatar kula da nagarta da rigakafin ta’addanci ta fitar a wannan makon.
Wani jami’in Taliban ya raba ainihin tsari a cikin harshen Pashto; duk da haka manyan shugabanni ba su tabbatar da sahihancin sa ba.

Lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid, bai musanta sahihancin umarnin ba, amma ya ce har yanzu ya na “kokarin samun bayanai” game da dokar.

Umarnin ya nakalto ayoyi da dama daga Alqur’ani da hadisai, game da bin duk abin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya umuaci musulmi su yi.

“Tsarin gemu aiki ne na dabi’a kuma Sunna (hanyar rayuwa da tafarki na shari’a) na dukkan Annabawa da Shari’ar Musulunci sun sha jaddada shi,” in ji umarnin.

Ministan yada kyawawan dabi’u, Sheikh Muhammad Khalid Haqqani ne ya sanya wa hannu kan wannan umarni.
“Aski ko yanke gemu haramun ne a karkashin shawarar da malaman addini su ka yi gaba daya. Sahabban Annabi Muhammadu (S.A.W) da mabiyansu da magadan bayansu da Mujahidai [Jarumai tsarkaka] da sauran malamai ba su yi ittifaqi a kan aske ko aski ba.

“Domin haka, an fahimci cewa aski ko yanke gemu ya saba wa dabi’ar dan Adam, kuma matakin ya saba wa Shari’ar Musulunci,” a cewar umarnin.

“Saboda abin da ya gabata, a na sanar da duk masu yin aski da su kiyaye Shari’ar Musulunci da umarnin Musulunci yayin yanke gashi da yi wa abokan cinikinsu hidima.”

Ga dukkan alamu wannan umarni ya tsaya cik kan dokar hana sassauta gemu da kungiyar Taliban ta bayar a lokacin gwamnatinsu ta karshe daga 1996 zuwa 2001. Jami’an Taliban sun ce kungiyar na kokarin karfafawa ‘yan kasar ta Afganistan kwarin gwiwa, wajen daukar tsauraran ra’ayin addinin Musulunci.
“Dukkan sassan larduna da ke karkashin ma’aikatar an umarce su da cewa, tsayar da gemu daya ne daga cikin Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.WA), kuma dukkan Musulmi su bi Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.W). Haka nan kuma an umarci dukkan ma’aikatan aski da ke larduna da su kiyaye umarnin yayin da su ke yanke gemu na kwastomomi.”
“Ya kamata jami’a su yi kokarin aiwatar da wannan dokar cikin ladabi da mutuntawa, domin haka ‘yan kasar su yi rayuwarsu daidai da addininsu, wajibcin Musulunci da Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.W)”. A cewar umarnin.

“An aiko muku da waɗannan umarnin, doMIn aiwatarwa.”
Sai dai kuma masu aski a Kabul sun ce mutane da yawa ba sa son aske gemu tun kafin Taliban ta fitar da wannan doka.
Wani mai aski a wani shagon Kabul ya shaidawa Muryar Amurka cewa, a farkon watan Disamba yak an yi aski kashi 20 cikin 100 na kasuwancin da ya ke yi a baya tun bayan da ‘yan Taliban su ka karbe birnin.

‘Yan Taliban sun kwace iko da babban birnin Afganistan a tsakiyar watan Agusta. Tun daga wannan lokacin suka fara gabatar da shari’o’in Musulunci tare da haramta cudanya da tarbiyyar maza da mata.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.



Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.



Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….



Continue Reading

Trending