Connect with us

Labarai

KAROTA ta yi nisa wajen gyara Babur din da a ka lalata a Kano

Published

on

Hukumar KAROTA na ci gaba da gyaran Baburan Adaidaita Sahun da bata garin da su ka lalata mu su ababen hawan su a lokacin da su ka fito aiki.

Gwamnan jihar Kano ne dai ya umarci hukumar da ta gyarawa duk wani dan Adaidaita Sahun da ya bi doka ya fito aiki, wasu kuma su ka lalata mu su Babur.

Wani daga cikin wanda a ka lalatawa Babur a yankin Rimin Kebe, ya ce”Ina tsaka da aiki nan a diban fasinja, matasa su ka fito da muggan mamakai su ka fasa min gilashi da fitulu, baya ga lallotsa min jikin Babur di na, wa su kuma a ka farfasa mu su tayoyi wanda yanzu haka duk an gyara mana”.

Tun da fari dai shugaban KAROTA, Baffa Baffa Dan Agundi, ya ce,”Jami’an tsaro sun shirya tsaf, domin bayar da kariya ga duk dan Adaidaita Sahun da ya bi doka ya fito aikin sa”.

A hannu guda kuma ya lashi takobin hukunta duk wanda a ka kama da laifin fasa Babur din Adaidaita.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending