Connect with us

Labarai

Mai yiwa ‘yan adaidaita lodi: Ina goyan bayan tafiya yajin aiki – Dattijo

Published

on

Wani dattijo da ya ke yiwa direbobin Adaidaita Sahu lodi ya bayyana goyon bayan daukar matakin yajin aikin.

Dattijon mai suna Inusa Uba mai kimanin shekaru 65 ya ce, ya na da mata biyu da ‘ya’ya 18 kuma da wannan sana’a ta lodin Adaidaita yake yin duk bukatun sa na yau da kullum.

Ya kuma ce, duk da halin kunci da su ka tsinci kan su a ciki sakamakon yajin aikin, amma dai matakin yajin aikin shi ne mafi sauki a wajensu.

Talata it ace rana ta biyu da ‘yan Adaidaita Sahu su ka tsunduma yajin aiki, saboda zargin hukumar KAROTA ta sa musu dokar sabunta lamba kan Naira Dubu Takwas.

Labarai

Rahoto: Dokar hana shan shisha ta fara aiki gadan-gadan a Kano – Hisba

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kai simamen shagunan da ake sayar da Shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano, inda ta samu nasarar kama dillalan Shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita.

A zantawar daya daga cikin masu shagunan sayar da Shisha da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, ya bayyana cewar, ya yi tunanin dokar hana shan Shisha ta tsaya kan masu wuraren shan Shisha ba masu sayarwa ba.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Shekaru 10 ina sarrafa Turoso amma ko ciwon kai ban taba yi ba – Mai Turoso

Published

on

Wani magidanci mai sana’ar sarrafa Turoso a yankin Kududdufawa ya ce, sama da shekaru goma ya na aikin sarrafa Turoso, amma ko ciwon kai bai taba yi ba.

Malam Isah Musa Katsinawa mazunin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Gobara ta lakume ran mutane 3 ciki harda dattijuwa

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, ta kai tallafi wani gida da aka samu iftila’in gobara, wanda ta yi sanadiyar rasa mutane Uku  a unguwar Gama A, da ke karamar hukumar Nasarawa.

Wakilin mu na ‘yan zazu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar, hukumar karkashin shugabanta Salihu Aliyu Jili, ta kuma kai tallafi gidan iyayen Hanifa, dalibar da aka yi zargin malaminta ya kashe ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending