Connect with us

Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: ‘Yar PSG ta lashe kyautar mai tsaron raga ta shekarar 2021

Published

on

Mai  tsaron ragar kungiyar kwallon kafa PSG ta kasar Faransa bangaren mata, Christiane Endler, ta lashe kyautar gwarzuwar mai tsaron raga ta shekarar 2021.

Endker ta kasance a baya, ta na gama na biyu sau biyu a jere kafin wannan karon ta zama ta daya. ‘Yan wasan mai shekaru 30, ta taimaka wa PSG ta lashe gasar Dibi 1 ta Mata a bara. An zura mata kwallaye hudu ne kacal a kakar wasa ta bana kuma an nada ta a matsayin mai tsaron ragar rukunin.

‘Yar wasan Jamus Ann-Katrin Berger ta taimaka wa Chelsea ta lashe gasar cikin kofin gida kuma ta lashe kyautar safar hannu ta Golden Glove a gasar, saboda yawan share fage fiye da kowane mai tsaron gida.

Labbe, wadda ita ce magajin Endler a ragar PSG, ta kasance mabudi ga kokarin da Canada ta yi na samun zinari a gasar Olympics ta lokacin bazara ta 2020, inda ta ci biyu kawai daga cikin fanareti shida a wasan karshe da suka yi da Sweden.

Manta Sabo

Kotu ta umarci CBN da ya sakarwa ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗen su.

Published

on

Babbar kotun jaha karkashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Musa Ƙaraye, ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN, da ofishin babban akanta na kasar nan daga yin jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da gwamnatin tarayya ke bayarwa.

Cikin wata ƙara wadda shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Kano da mutane shida amadadin ƙungiyar suka shigar.

Waɗanda ake karar dai a gaban kotun sun hadar da babban akanta na kasar nan da kuma babban bankin Najeriya CBN, sai kuma wasu bankuna guda 7 da dukkanin ƙananan hukumomin Kano.

Masu ƙarar ta bakin lauyan su Barrister Bashir Yusuf Tudun Wuzurci, sun bayyana wa kotun cewar idan aka hana ƙananan hukumomin kudadensu hakan zai haifar da koma baya a jahar Kano kuma yin hakan ya saɓawa doka.

Kotun ta amince da dukkan roke-roken masu karar inda aka kùma ayyana cewar kodai babban bankin ƙasa CBN, ko babban akanta na kasar da ragowar waɗanda aka yi karar ko yan korensu cewar kada su yi jinkiri wajen biyan ƙananan hukumomin Kano kudadensu na arzikin kasa da ake rabawa kowace karamar hukuma.

Kotun ta kuma yi umarni da a aikewa waɗanda ake ƙara kwafin umarnin da ta bayar.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar kotun ta sanya ranar 21 ga wannan watan dan sauraren kowanne ɓangaren.

Continue Reading

Manyan Labarai

Muna Allah wa-dai da tsare yaran da gwamnatin tarayya ta kama yayin zanga-zangar tsadar rayuwa  – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta yi Allah wa-dai da matakin gabatar da matasa da yaran nan a gaban kotun tarayya da ke Abuja, waɗanda aka kama a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, a Kano, da Jos da Kaduna.

Gwamnatin tarayya dai tana zargin waɗanda aka kama ɗin ne da zargin cin amanar ƙasa, bayan da take zargin an same su suna ɗaga tutocin ƙasar Rasha a zanga-zangar kawo ƙarshen yunwa da aka gudanar a tsakanin 1 zuwa goma ga watan Agustan 2024.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya shaidawa Dala FM Kano cewar, babu adalci a gabatar da matasan a gaban kotun, kasancewar mafi yawancin su ƙananan yara ne har da ƴan shekaru 14, da 15, da kuma ƴan shekaru 18.

Tasi’u Soja, ya kuma ce tsare yaran da aka yi kusan watanni uku babu adalci a cikin lamarin, yana mai cewa za su yi duk mai yiyuwa don ganin an yiwa yaran adalci.

“Muna kira ga Ƴan Majalisun Arewa, da Sarakuna, da Ƴan Siyasar Arewa da su yi gaggawar ganawa da fadar shugaban ƙasa domin sakin yaran nan duba da take musu haƙƙi da aka yi, “in ji Tasi’u”.

Rahotanni sun bayyana cewar ana tsaka da shari’ar yaran ne a ranar Juma’a 01 ga watan Nuwamban 2024, sai hudu daga cikin su suka faɗi magashiyyan lamarin da mai shari’ar Oboira Egwyatu ya dakatar da shari’ar don duba yaran.

Kotun dai ta sanya yaran a hannu belin ajiye Naira Miliyan goma-goma kowannen su, tare da wanda zai tsayawa kowannen su mai matakin albashi 15, lamarin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin ta ƙalubalanci sharuɗan belin kasancewar ya yi tsauri da yawa tare da rashin adalci a ciki.

A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar iyayen yaran da aka gabatar a gaban kotun tarayya da ke Abuja, Nura Ahmad Muhammad, ya ce talaucin iyayen yaran da kuma rashin kishin ƴan siyasa da masu fada a ji ne yasa ake tuhumar yaransu da laifukan da basu aikata ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gundura da ake zargi da sarewa Ɗan Bijilante hannu da fasa motar ƴan sanda ya shiga hannu

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wani Matashi mai suna Inuwa Zakari ɗan shekara 24, wanda akafi sani da Gundura, wanda ake zargi da sarewa wani Ɗan Bijilante hannu, da kuma fasa motar Ƴan Sanda, da wasu Laifuka

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM a daren Litinin, Kiyawa ya ce Matashi Gundura sun daɗe suna neman sa ruwa a jallo bisa zargin sa da tarin Laifuka.

“Gundura ya kasance abokin fitaccen ɗan Dabar nan Abba Burakita ɗa unguwar Ɗorayi da ya rasu a baya, kuma har kotu ma muka gurfanar da shi daga baya ya fita amma bai dai na abinda ya ke yi ba, a ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano, da ya shigo yana yunƙurin tayar da hankalin al’umma jami’an mu suka kama shi, “in ji SP Kiyawa”.

Har ila yau, Abdullahi ya ce an kama Gundura da wukake guda biyu a wani waje na matattarar Yan Daba da suke kira “Jungle” a Unguwar Dorayi.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta kuma cafke ƙarin wasu matasa 14, da ake zargin su da aikata maban-banta laifuka, inda aka kama su a tsakanin 25 ga zuwa 27 na watan Oktoban 2024.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka waɗanda ake zargin ana ci gaba da bincike a kan su a babban sashin binciken manyan laifuka na CID, da ke hedikwatar rundunar da ke Bompai a Kano, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a gaban kotu.

Continue Reading

Trending