Connect with us

Lafiya

Korona: Jamus ta tabbatar da mutuwar mutane dubu 112,323

Published

on

Kasar Jamus ta tabbatar da kamuwar mutane 112,323 a ranar Laraba, a sabon alkaluman kwana guda yayin da ministan kiwon lafiya ya ce, ba a kai kololuwar ba kuma ya kamata a bullo da allurar rigakafin a watan Mayu.

Adadin cututtukan COVID-19 na Jamus a yanzu ya kai 8,186,850, in ji Cibiyar Robert Koch (RKI) domin kamuwa da cutar. Adadin wadanda suka mutu ya kuma karu da 239 a ranar Laraba ya kai 116,081.

Ministan lafiya Karl Lauterbach, ya ce, ya na sa ran guguwar za ta yi tashin gwauron zabi a cikin ‘yan makwanni kamar yadda bambance-bambancen Omicron mai saurin yaduwa ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar ta Jamus tsawon kwanaki bakwai zuwa 584.4 a cikin mutane 100,000.

“Ina tsammanin za mu kai kololuwar girgizar a tsakiyar watan Fabrairu, sannan adadin wadanda suka kamu da cutar na iya sake faduwa, amma har yanzu ba mu kai ga kololuwa ba,” in ji Lauterbach ga gidan rediyon RTL da yammacin ranar Talata.

Lauterbach ya ce, ya yi imanin cewa, adadin kararrakin da ba a bayar da rahoton ba na iya kusan sau biyu girma fiye da sanannun alkaluma.

Ya ce, ya kamata a bullo da allurar riga-kafi cikin sauri, a cikin Afrilu ko Mayu, domin guje wa sake kamuwa da cutar tare da yiwuwar sabbin bambance-bambance a cikin kaka.

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Lafiya

Za’a yiwa kusan yara miliyan 3 rigakafin cutar shan Inna a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace kusan Yara miliyan 3 za’ayiwa rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin jihar nan 44, duba da samun ɓurɓushinta da kaso 65, a jihar ta Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rigakafin cutar shan innar a yau Alhamis, wanda za’a kwashe kwanaki 4 ana gudanarwa a Kano.

Dakta Abubakar Labaran ya ce duba da shigowar zafin akwai buƙatar al’umma su kula da alamomin cutar sankarau, duk da gwamnati ta yi shirin bayar da agajin gaggawa, kamar yadda tashar Dala FM Kano ta rawaito.

Ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano dai ta ce za’a ci gaba da gudanar da sauran rigafin, domin bai wa yaran jihar Kano kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Continue Reading

Lafiya

Dokar tilasta gwajin lafiya kafin aure ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano

Published

on

Rahotanni na bayyana cewar majalisar dokokin jihar Kano, ta yi karatu na biyu a kan kudirin dokar tilasta wa masu niyyar yin aure yin gwajin cutar kanjamau, da na cutar hanta da kuma duba kwayoyin jini wato Sikila, gabanin daura aure.

Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Hon.Musa Ali Kachako, shin wanda ya kawo kudirin dokar, ya bayyana cewa, jihar Kano na fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka hada da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba, hakan ne ma ya sa ya kai ƙudirin.

Kachako, ya ce, ƙudirin dokar idan har aka amince da shi, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaɗuwar cututtuka masu barazana ga rayuwar al’umma, kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito.

Da yake nuna goyon bayansa kan ƙudirin Ɗan majalisa Hon. Aminu Sa’ad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce, jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar, domin kare lafiyar ‘yan jiharta ta hanyar samar da gwaje-gwaje kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka, kamar cutar hanta, da sauran cututtuka.

Continue Reading

Trending