Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Fireminista Birtaniya Boris na ci gaba da shan matsi ya sauka daga mukamin sa

Published

on

Firayim Ministan Biritaniya, Boris Johnson, ya na shan matsi da daga ‘yan majalisar dokokin da suka fusata kan jerin kulle-kulle na Korona da ya karya ka’ida a Downing Street.

Johnson ya sha neman afuwar jam’iyyun kuma ya ce, bai san da yawa daga cikinsu ba. Koyaya, ya halarci abin da ya ce, ya na tsammanin wani taron aiki ne a ranar 20 ga Mayu, 2020.

Domin haifar da ƙalubalen shugabanci, 54 daga cikin 360 ‘yan majalisar masu ra’ayin mazan jiya a majalisa dole ne su rubuta wasiƙar rashin amincewa ga shugaban kwamitin jam’iyyar na 1922.

Kimanin ‘yan majalisar masu ra’ayin mazan jiya 20 da suka ci kujerunsu a zaben kasar da ya gabata a shekarar 2019 sun shirya mika wasikun rashin amincewa ga Johnson, in ji jaridar Telegraph. Wasu tsiraru sun riga sun ce sun rubuta irin waɗannan wasiƙun.

Ƙasashen Ƙetare

Saudiyya ta sanar da Litinin a matsayin ranar Sallar Idi ƙarama

Published

on

Kasar Saudiyya ta ce, ranar Litinin 2 ga watan Mayu a matsayin ranar Eid-el Fitr saboda ba a ga watan Shawwal ba.

Sanarwar ta ce, ba a iya ganin jinjirin watan Shawwal ba daga dakin kallo na Tamir ko kuma na jami’ar Majmaah da ke Hautat Sudair a ranar Asabar.

A cewar jaridar Saudi Gazette, hakan na nufin ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, ita ce ranar karshe ta watan Ramadan, kuma ranar Litinin 2 ga watan Mayu, ita ce ranar farko ta Idin sallah ƙarama ta Al-Fitr.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Jack Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3 bayan Elon Musk ya mallaki shafin Twitter

Published

on

Wanda ya kafa kuma tsohon Shugaban Kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya samu zunzurutun kudi har Naira Biliyan 405.3, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 977.8, bayan attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk, ya mallaki kamfanin sadarwar a ranar Litinin.

Hukumar ta Twitter ta gana da Musk da sanyin safiyar ranar Litinin, amma an tabbatar da amincewa da yarjejeniyar daga baya a ranar ta hannun hamshakin dan kasuwar.

Musk ya mallaki Twitter da sama da dala biliyan 43, bayan da ya samu dala biliyan 46.5 daga bankuna, domin samar da kudaden shiga. Shugaban Tesla da SpaceX ya na da darajar dala biliyan 268.2 har zuwa Afrilu 25, 2022.

Bayan kammala sayan, Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3, dangane da farashin canjin kasuwa na hukuma daga yarjejeniyar, yayin da Musk ya biya dala 54.20 ga masu zuba jari da ke rike da hannun jarin Twitter.

Dorsey ya mallaki hannun jari miliyan 18.04 a shafin Twitter kafin ya fice daga mukaminsa na shugaba a watan Nuwambar bara, abin da ya sa ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari goma a dandalin sada zumunta kafin sayen.

Dorsey shine mutum na 356 mafi arziki a duniya. Forbes ta kiyasta darajarsa a kan dala biliyan 6.8, kuma a halin yanzu ya na shugabancin Block, wanda a da ake kira Square, wani kamfani na biyan kuɗi a Amurka. A cewar Ripple Nigeria.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Askarawa sun kama tarin nakasassun bogi na yin bara a masallacin Ka’aba

Published

on

Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mazauna birnin da wadanda suka kama suna bara a kusa da masallacin Ka’aba.

Hukumomin sun ce, sun kama wani dan kasar Indiya, saboda an kama shi ya na kokarin karkatar da hanun masu ibada, domin su ba shi kudi, sannan sun damke wani dan asalin kasar Morocco da yake bara a jikin wata kofar shiga masallacin Ka’aba.

Akwai kuma wani dan kasar Yemen wanda ke amfani da sandunan guragu, domin yaudarar masu ibada cewa, shi mai nakasa ne.

A cewar BBC, an kama wani mutum da ke tura dansa ya yi bara ta hanyar saka shi a kan keken guragu. Bincike ya tabbatar cewa dan nasa kalau yake.

Hukumar da ke kula da tsaron al’umma ta Saudiyya ta sanar cewa, duk wanda aka kama yana bara, ko kuma wanda ya iza wani ya yi bara, ko ma ya amince da yin barar, zai shafe kusan shekara guda yana zaman gidan kaso ko ya biya tarar Riyal 100,000 ko ma duka.

Continue Reading

Trending