Connect with us

Labarai

Ali Nuhu ya tsoma baki a diyyar da ake nema a hannun Hafsat Idris

Published

on

Jarumi kuma mai bada umarni a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Ali Nuhu, ya shiga tsakanin jaruma Hafsat Idris da wani kamfani UK Entertaiment  har an samu sasanci, a babbar kotun jihar Kano, karkashin mai shari’a Zuwaira Yusuf.

Lauyan kamfanin ya bayyana a gaban kotun ranar a ranar Litinin 24-01-2022, domin ci gaba da shari’ar, sai dai ya shaida cewar, sun rufe karar biyo bayan sasanci da aka samu a tsakanin su da jarumar.

Tun abaya dai kamfanin, ya shigar da jarumar kara kan cewar, sun yi jarjejeniyar za ta yi masa wani aiki na TV Shoamw, a kan kudi Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Uku, amma ta tsere, lamarin da ya sa su ka yi karar ta a gaban kotu.

Kamfain ya nemi ta biya su Naira Miliyan Goma a matsayin kudin damejin da ta yi musu, ta hannun lauyansu Ibrahim Abdulkadir Chedi.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending