Connect with us

Labarai

Ganduje ya sanya ido tare da bin ka’idoji na sabunta lasisin makarantu kudi – PDP

Published

on

Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano, ta ja hankalin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, cewa kar ya sake ya yi amfani da batun soke lasisin makarantu masu zaman kansu wajen tatsar kudade daga masu makarantun da sunan sake tsarin makarantun.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Shehu Wada Sagagi, wadda a ciki take nuna alhinin ta bisa kisan Hanifa da Abdulmalik Tanko ya kashe ta.

Jam’iyyar ta kuma yaba wa jami’an tsaro kan yadda su ka yi saurin ganowa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kotu.

Sai dai ta ce, a kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar, sakamakon abin da ya faru a kan yarinyar, jam’iyyar hamayyar ta ce, duk da cewa, abu ne da ya ke da kyau sake tsrain makarantun, to amma ta yi gargadi ga gwamnatin da kar ta yi amfani da wannan dama wajen tsatsar kudade daga masu makarantun.

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren.

Labarai

Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Published

on

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9

Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.

Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Published

on

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.

Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Babban Labari: Mun kama mota makare da kayan fashewa da bindugu da harsashi a Kano – Kiyawa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sami nasarar cafke wata mota makare da wasu kayayyakin da ake hada abubuwan fashewa da kuma bindigu kirar AK47 .

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, sun samu nasarar kama motar kirar Mercedez a unguwar Bubbugaje dake karamar hukumar Kumbotso.

A cewar Kiyawa sun sami rahoran sirri ne akan motar wadda suke zargin an kawo ta daga Jihar Jigawa zuwa Kano makare da irin kayayyakin da suke zargin da sune ake hada abubuwan fashewa domin aikata ta’addanci.

Sanarwar ta kuma ce bayan samun rahotan sirri na kara sowar motar zuwa Kano, jami’an tsaron Puff Adder suka yi wa mator kawanya, wanda hakan yasa mutanan ciki suka tsere suka bar motar a nan.

“Mun samu nasarar gano bindiga kirar AK47 guda biyu da kuma kananan bindigu biyu kirar Pistol tare da alburusai dubu daya da dari takwas”. In ji Kiyawa.

Continue Reading

Trending