Connect with us

Labarai

Da Dumi-Dumi: Kotu ta aike da tsohon kwamishina gidan gyaran hali bisa zagin Ganduje

Published

on

Kotun Majistret mai lamba 58 karkashin jagorancin mai shari’a, Aminu Gabari, ta aike da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji gidan ajiya da gyaran hali.

A na tuhumar Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya bisa zargin bata suna da cin mutuncin Gwamnan Kano da iyalan sa.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar, wani lauya ne mai suna, Adekunle Taiwo, ya shigar da kara a madadin gwamnan Kano a kan cewar, Dan Sarauniyar ya sanya wani hoto a shafinsa na Facebook wanda kuma sanya wannan hoto cin mutunci ne ga gwamnan Kano Ganduje.

Yayin da aka karanta masa tuhumar ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da a ke yi masa.

Lauya mai gabatar da kara, Wada A Wada ya roki kotun da ta sanya wata ranar dan su gabatar da shaida.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Barista Garzali Datti Ahmad, shi ne lauyan wanda ake tuhuma ya roki kotun da ta sanya Dan Sarauniyar a hannun beli ya kuma tallafi rokon da sashi na 35 da na 36 (5) na kundin tsarin mulkin kasa, ya kuma tallafi rokon da sashi na 168 da na 172 da kuma sashi na 172 na kundin tafikar da shari’ar ACJL 2019.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending