Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Dattijon da aka yi wa dashen zuciyar Alade ya mutu

Published

on

Mutumin da a ka yi wa dashen zuciyar Alade a kasar Amurka ya mutu bayan watanni biyu da yi masa aikin dashen zuciyar.

David Bennett mai shekaru 57 da ke fama da ciwon zuciya, tun a cikin watan Janairu, likitocin da ke Jami’ar Maryland (UMSOM) su ka yi masa dashen.

Amma a ranar Talata, asibitin ya ba da sanarwar cewa David Bennett ya mutu, in ji Sky News.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwarsa ba, amma likitocin sun ce ciwon nasa ya na kara tabarbarewa tsawon kwanaki.

A halin da ake ciki, dan Bennett, David Jr, ya yabawa asibitin bisa yunkurin yi wa mahaifinsa tiyatar, domin ceto ran mahaifinsa, ya kuma ce iyalansa na fatan hakan zai taimaka a kokarin da ake na magance karancin sassan dashen.

Kafin a yi masa dashen a watan Janairu, an kwantar da marigayin a asibiti, kuma ya kwanta a gado na tsawon watanni kuma an haɗa shi da na’urar kewayawa ta huhu domin ci gaba da raye.

An ba da rahoton cewa dashen shine zaɓi ɗaya tilo ga mara lafiyar da aka ce yana fama da cutar arrhythmia mai barazana ga rayuwa.

An ba da rahoton cewa ba zai cancanci yin dashen zuciya na yau da kullun ba a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Maryland (UMMC) da sauran manyan cibiyoyin dashen dashen da suka yi bitar bayanan lafiyarsa.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending