Manyan Labarai
Champions League: Liverpool da Man City za su tinkari kungiyoyin Andulisiya

Manchester City da Liverpool za su tunkari kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai Champions League, wanda za su tunkari kungiyoyin kasar Andulusiya a gasar.
City na fatan za ta fi na bara bayan ta sha kashi a wasan karshe a hannun Chelsea yanzu kuma za ta tinkari Real Madrid wadda ke kan gaba a gasar Laliga.
Haka kuma Liverpool na fuskantar hamayyar LaLiga, duk da cewa da wuya Villarreal ta samu kai banten ta da take tsammanin haduwa a wannan matakin na gasar.
Wanda kwararre a fagen kwallon kafa a Unai Emery ke jagoranta, Villarreal za ta yi wasa da Liverpool.
Labarai
Rahoto: Dalibi ya kawo credit 9 a qualifying ya yi tsauri da yawa – Mai duba jarabawa

Wani tsohon mai duba sakamakon jarabawar qualifying a jihar Kano ya ce, ana duba gazawar biyawa dalibai kudin jarabawar qualifying ne yayin fitar da sakamako, saboda haka akwai rashin adalci akan lallai sai dalibai sun kawo credit 9
Tsohon mai duba sakamakon jarabawar, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.
Labarai
Rahoto: Yadda hadarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a Lambu

Wasu motoci babba da karama, sun yi taho mu gama akan titin garin Lambu da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu, daya kuma ya jikkata.
Wasu da al’amarin ya faru a gaban idanunsu, sun bayyanawa wakilin mu na ‘yan Zazu , Abubakar Sabo cewar, mai karamar motar ne ya yi a ran hannu, wanda ya janyo faruwar hadarin.
Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.
Manyan Labarai
Da Duminsa: Klopp ya taya Guardiola murnar lashe Firimiya

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, bisa lashe gasar kofin Firimiyar kasar Ingila da ta yi a kakar bana.
Manchester City ta lashe kofin Firimiya ne da maki daya kacal a kan Liverpool, wanda aka karkare gasar Man City na da maki 93 Liverpool na da maki 92.
“Ina taya ku murna ga Man City da Pep Guardiola, na gode wa Aston Villa da Wolverhampton, saboda yadda suka yi wasa mai kyau.”
“Ba sakamakon da muke so ba ne, dan wasan ne. Ban san ainihin sakamakon ba amma na san sun tashi 1-0 – shin sun tashi 2-0 kuma? Tabbas a halin yanzu akwai rashin jin daɗi. nan ma.
“Idan aka tashi 5-0 a City bayan mintuna 10 wasa ne kawai a gare mu. Ba wasanmu mafi kyau ba ne, amma duk yana da kyau.
-
Nishadi2 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai2 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai2 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Manyan Labarai2 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari