Manyan Labarai
Mun kammala shiri domin bayar da katin zabe – INEC

Kwamishinan Zabe na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Jihar Oyo, Dr Mutiu Agboke ya bayyana cewa sama da katunan zabe na dindindin (PVCs) 45,000 sun kammala domin karbar su.
Mrs Rosemary Adeniyi, Shugabar Sashen Ilimi da Yada Labarai na Hukumar a Oyo ta rawaito Agboke ya na bayyana hakan a ranar Litinin a Ibadan.
A cewarta, Agboke ta ce, katinan zabe na PVC na masu kada kuri’a ne da suka yi rijista a kashi na daya da na biyu na ci gaba da rijistar masu kada kuri’a (CVR) tsakanin 28 ga watan Yuni zuwa Disamba 2021.
Ya kuma bukaci mutanen da suka yi rijista da su ziyarci ofisoshin hukumar a fadin kananan hukumomi 33 na jihar domin karbar katin su.

Manyan Labarai
Fadan dabar kofar Na’isa da kofar Dan-agundi, laifin iyaye – Mazaunin Yankin

Wani mazaunin ƙofar Na’isa wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce faɗan dabar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin da Ɗan Agundi, laifin iyaye ne, da kuma wasu manya a unguwannin da ake zargin suna goya musu baya ta hanyar daƙile yunƙurin hukumomi na ɗaukar doka a kansu.
Mutumin ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, biyo bayan yadda rikicin faɗan dabar ya sake ɓarkewa a unguwannin a Alhamis ɗin nan, al’amarin da ya janyo asarar dukiyoyin al’umma a yankunan.
Ya ce lamarin ya faro ne tun a lokacin bikin ƙaramar Sallah, lamarin da a baya ƙura ta lafa, sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sai gashi an sake samun faɗan dabar.
A cewar sa, “A lokacin faɗan dabar ya faru an Sassari mutane da dama, hatta Saniya ma ba ta tsira ba sai da aka sareta, tare da fasa gilasan ababen hawan Mutane, “in ji shi”.
Sa dai mutumin ya ce, tuni jami’an tsaron Ƴan Sanda, suka kai ɗauki tare da kwantar da tarzoma, lamarin da ƙurar ta lafa.

Manyan Labarai
Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.
Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.
“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.
Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.
Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.
Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.
Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su