Connect with us

Ƙasashen Ƙetare

Jack Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3 bayan Elon Musk ya mallaki shafin Twitter

Published

on

Wanda ya kafa kuma tsohon Shugaban Kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya samu zunzurutun kudi har Naira Biliyan 405.3, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 977.8, bayan attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk, ya mallaki kamfanin sadarwar a ranar Litinin.

Hukumar ta Twitter ta gana da Musk da sanyin safiyar ranar Litinin, amma an tabbatar da amincewa da yarjejeniyar daga baya a ranar ta hannun hamshakin dan kasuwar.

Musk ya mallaki Twitter da sama da dala biliyan 43, bayan da ya samu dala biliyan 46.5 daga bankuna, domin samar da kudaden shiga. Shugaban Tesla da SpaceX ya na da darajar dala biliyan 268.2 har zuwa Afrilu 25, 2022.

Bayan kammala sayan, Dorsey ya samu Naira biliyan 405.3, dangane da farashin canjin kasuwa na hukuma daga yarjejeniyar, yayin da Musk ya biya dala 54.20 ga masu zuba jari da ke rike da hannun jarin Twitter.

Dorsey ya mallaki hannun jari miliyan 18.04 a shafin Twitter kafin ya fice daga mukaminsa na shugaba a watan Nuwambar bara, abin da ya sa ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari goma a dandalin sada zumunta kafin sayen.

Dorsey shine mutum na 356 mafi arziki a duniya. Forbes ta kiyasta darajarsa a kan dala biliyan 6.8, kuma a halin yanzu ya na shugabancin Block, wanda a da ake kira Square, wani kamfani na biyan kuɗi a Amurka. A cewar Ripple Nigeria.

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji Sun yi juyin Mulki a Gabon

Published

on

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.

Sun Kuma ce Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, “Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu.”

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Sojoji sunyi juyin Mulki a jamhuriyar Nijar

Published

on

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa Sojojin Kasar sun yi juyin Mulki, tare da sanar da kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum.

Cikin sanarwar da suka bayar a gidan telebijin din Kasar, jagoran tawagar sojojin Kanal Amadu Abdramane yace “mun kawo karshen mulkin shugaba Muhammad Bazum tare da karbe dukkanin Wani Iko”.

Sojojin dai sun bayar da dalilin halin rashin tabbas da Kuma Matsin tattalin arziki a kasar.

Tuni dai sojojin suka garkame dukkanin iyakokin Kasar tare da Sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Tun a safiyar laraba ne dai aka wayi gari da fara wancan yunkuri, Wanda yanzu haka ta tabbata, Kasar Nijar na hannun sojoji, Wanda shi ne Karo na hudu ana gudanar da juyin mulkin a jamhuriyar Nijar.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

An tsaurara tsaro a fadar shugaban Kasar Nijar

Published

on

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasa sun rufe duk wata hanyar shiga fadar a wani lamari da ba a kai ga ganowa ba.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu daga cikin tsofaffin shugabannin ƙasar ta Nijar na tattaunawa da sojojin domin sasanta lamarin.

Karin bayani nan tafe….

Continue Reading

Trending